An Lakaɗawa Kansila Duka kan Zargin ba Shi Kuɗi Ya Mari na kusa da Gwamna
- Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda ake kifawa wani kansila maruka saboda wasu zarge-zarge
- Matashin da ake zargin hadimin shugaban ma’aikatan gwamnatin Gombe ne ya yi ta marin kansilan Shamaki ba adadi
- A bidiyon, an ji matashin cikin fushi yana kalubalantar kansilan cewa wai zai mari mai gidansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya tayar da hankula inda aka gano ana dukan kansila.
Bidiyon ya nuna mutumin da aka ce hadimin shugaban ma’aikatan gwamnatin Gombe yana cin zarafin kansilan Shamaki.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani bidiyo da ya bazu wanda Abdullahi Ghalee Illela ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren jiya Alhamis 18 ga watan Disambar 2025.
Yadda aka ta dukan kansila a Gombe
Bidiyon, mai tsawon minti daya da dakika 29, ya nuna matashin mai suna Adamu Danko yana mari da naushin kansilan yayin da yake masa tambayoyi cikin fushi.
Shi kuma kansilan cikin rauni yana ƙoƙarin kwantar da tarzoma ta hanyar neman afuwa da roƙon a bar maganar.
Sai dai duk da kaskantar da kansa da ya yi, Danko ya ci gaba da naushi har da gwarel da kai.
Lamarin ya jawo martani daga jama’a, inda da dama suka yi Allah-wadai da abin da ya faru tare da neman a hukunta wanda ake zargi.
Har yanzu hukumomi ba su tabbatar ko musanta zargin ba, sai dai masu sharhi na kira ga shugaban ma’aikatan jihar da gwamnatin jihar su nesanta kansa.

Source: Facebook
Lauya ya tsoma kansa cikin rigimar
A wani bangaren, wani lauya Ahmed Ahmed Yerima ya bayyana aniyarsa ta tsayawa Dan Buba watau Kansilan Shamaki kan abin da ya faru, kamar yadda Ahmad Abdulahi Deputy ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023
Lauyan ya bayyana lamarin a matsayin abin Allah-wadai da kuma saba wa ka’idojin doka, yana mai jaddada cewa babu wanda ya fi karfin doka.
Ya lashi takobin amfani da dukkan hanyoyin shari’a da suka dace domin tabbatar da an gudanar da cikakken bincike, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Yerima ya kuma bukaci al’umma da su mara wa wannan kira na adalci baya ta hanyar yadawa da wayar da kai, yana mai cewa shiru na kara karfafa zalunci.
A cewarsa, dole ne a nemi gaskiya, a tabbatar da adalci, kuma a mutunta doka domin zaman lafiya da daidaito su dore a cikin al’umma.
Zamfara: An yi wa dan majalisa ruwan duwatsu
Kun ji cewa wani bidiyo ya nuna wasu fusatattun mutane sun tayar da kura a garin Dansadau da ke Zamfara, bayan sun yi wa dan majalisar mazabarsu ruwan duwatsu.
Mutanen sun zargi dan majalisar da rashin ziyartar mazabarsa, rashin jajanta wa wadanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a yankin.
A cikin wani bidiyo, an gano yadda mutane suka rika jifar dan majalisar, har da marinsa, suna ihun 'ba ma yi'.
Asali: Legit.ng
