Akpabio Ya Goyi Bayan Kashe 'Yan Bindiga Masu Garkuwa da Mutane

Akpabio Ya Goyi Bayan Kashe 'Yan Bindiga Masu Garkuwa da Mutane

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya nuna cikakken goyon baya ga hukuncin kisa a kan masu garkuwa da mutane
  • Ya yaba da jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tsaro, musamman ceto daliban da aka sace a baya-bayan nan a makarantu
  • Wani rahoto ya ce Sanata Akpabio ya ce APC na kara ƙarfi, tare da alƙawarin haɗa ƙuri’u domin nasara a zaben 2027 mai zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana matsayinsa a fili kan batun hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane.

Shugaban ya yi magana yana mai cewa hakan na daga cikin matakan da suka dace domin dakile laifuffuka masu girma a ƙasar nan.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya
Sanata Godswill Akpabio yayin wani zama a majalisa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Akpabio ya bayyana hakan ne a taron manyan ’yan jam’iyyar APC na kasa karo na 14 da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Sarki ya hada tawaga zuwa wajen Tinubu, sun goyi bayan tazarcensa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Goyon bayan hukuncin kisa ga masu garkuwa

A jawabin da ya gabatar, Akpabio ya ce a shirye majalisar dattawa take ta mara wa matakan da za su ƙarfafa tsaro, ciki har da hukuncin kisa ga masu aikata garkuwa da mutane.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa an daidaita laifin garkuwa da mutane da ta’addanci a cikin sababbin matakan doka da aka dauka

A cewarsa, idan shugaban kasa ya amince da kudurin da aka gabatar, duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane zai fuskanci hukuncin kisa.

Tinubu, Akpabio a taron APC a Abuja
Shugaba Bola Tinubu, Godswill Akpabio da manyan APC yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya yi gargadi cewa rashin aiwatar da hukunci mai tsauri na iya ƙara janyo ficewar masu laifi daga gidajen yari da kuma ci gaba da kashe-kashe.

Godswill Akpabio ya yaba wa Bola Tinubu

Akpabio ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa abin da ya kira jagoranci mai kyau wajen fuskantar matsalolin tsaro a kasar nan.

Ya jinjina wa gwamnatin tarayya kan nasarar ceto daliban da aka sace, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa.

Kara karanta wannan

Jita jitar mutuwar Akpabio ta harzuka majalisa, ta dauki mataki

Sanata Akpabio ya kuma yi addu’a domin dawo da sauran daliban da har yanzu ke hannun masu garkuwa, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan sojoji da fararen hula da suka rasa rayukansu.

Punch ta rahoto cewa ya yaba da rawar da Tinubu ya taka wajen tallafa wa dimokuraɗiyya a jamhuriyar Benin, yana mai cewa rashin kwanciyar hankali a makwabta na iya shafar Najeriya kai tsaye.

Akpabio ya ce APC na shiri kan 2027

A bangaren siyasa, Akpabio ya bayyana cewa jam’iyyar APC na kara samun karɓuwa a jihohi daban-daban, musamman bayan shigowar wasu gwamnoni.

A karshe, Akpabio ya bayyana kwarin gwiwar cewa haɗin kai da ƙarfafa APC za su haifar da ƙuri’u masu tarin yawa, yana mai cewa hakan zai kai ga nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

An yi zanga-zanga kan tsaro a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar 'yan kwadago ta yi zanga-zanga kan matsalolin tsaro da suka jawo sace dalibai a jihohi.

Daruruwan ma'aikata ne suka fito kan tituna a jihohi daban-daban da suka hada da Gombe, Kano, Sokoto, Legas da sauransu.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu na amfani da EFCC wajen kama 'yan adawa a Najeriya?

Shugabannin kwadago sun ce lokaci ya yi da za su daina karbar uzuri daga gwamnati kan kashe-kashe da ake yi ba dare ba rana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng