Nuhu Ribadu Ya Gargaɗi Gwamnoni game da Tsaro a Bukukuwan Kashen Shekara

Nuhu Ribadu Ya Gargaɗi Gwamnoni game da Tsaro a Bukukuwan Kashen Shekara

  • Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) ya gargadi gwamnonin jihohi su ƙara tsaurara tsaro yayin bukukuwan ƙarshen shekara ta 2025
  • Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta tabbatar da shirin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin kare jama’a da dukiyoyinsu a wannan lokaci
  • ’Yan sanda a Abuja da Kebbi sun tura dubunnan jami’ai domin tabbatar da zaman lafiya a wuraren ibada, manyan hanyoyi da duk inda ake samun taruwar jama’a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) ya aike da saƙo ga gwamnonin jihohin Najeriya game da tsaron rayuka.

Ofishin ya bayar da umarni da a ƙara shiri da tsaurara matakan tsaro gabanin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Shugaban Majalisa, Akpabio ya ambato masu hana Najeriya zaman lafiya

Nuhu Ribadu ya gargadi gwamnoni
Wasu daga cikin daga cikin gwamnonin Najeriya Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na zuwa ne sakamakon yawaitar tafiye-tafiye, tarukan jama’a masu yawa da kuma ƙarin barazanar tsaro a wannan lokaci.

Gwamnoni sun karbi sakon Nuhu Ribadu

Daily Post ta wallada cewa umarnin na kunshe a cikin sakon da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta fitar bayan kammala taronta na bakwai a shekarar 2025, wanda aka gudanar a Abuja.

Sanarwar ta samu sa hannun Shugaban NGF kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq kuma Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun ne ya karanta.

Gwamnoni sun bayar da tabbacin tsaro a Najeriya
Mai ba Shugaban Kasa shawara kan tsaro Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

A cikin sanarwar, NGF ta ce ta karɓi wasiƙa daga ONSA da ke neman ƙara shirin tsaro a dukkannin jihohi yayin bukukuwan ƙarshen shekara ta 2025.

Gwamnonin sun jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, kare muhimman gine-gine da kayayyakin more rayuwa.

Haka kuma sun yi alkawarin tabbatar da bayyanar jami’an tsaro a wuraren da aka gano a matsayin masu haɗari, domin samun bukukuwa cikin kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

2027: An gyara dokokin zaben Najeriya a zauren majalisar wakilai

Gwamnoni sun fadi sakamakon gasar lafiya

Kungiyar gwamnonin sun bayyana sakamakon gasar karramawar jagorancin kula da lafiya a matakin farko (PHC) karo na uku da aka gudanar a ranar 12 ga Disamba 2025.

Jihar Yobe ce ta zama ta farko a ƙasa baki ɗaya, yayin da Zamfara, Nasarawa, Abia, Ribas da Osun suka yi fice a yankunansu.

Jihohin Kwara, Gombe, Kaduna, Anambra, Bayelsa da Ogun sun zo na biyu. Gwamnonin sun amince cewa nasarorin sun nuna muhimmancin jagoranci nagari tare da alƙawarin ƙara inganta lafiyar farko a ƙasa.

A wani ɓangare kuma, rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya (FCT) ta tura jami’ai 2,202 domin tsare wuraren ibada, wuraren shakatawa, manyan hanyoyi, tashoshin mota da sauran wuraren taruwar jama’a.

Kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta ce wannan na cikin umarnin ayyukan tsaro na bukukuwan 2025, tare da ƙara sintiri na leƙen asiri da bayyanar jami’ai a fili.

An taso Nuhu Ribadu a gaba

Kara karanta wannan

Shugaban Ƙasa, gwamnoni da ciyamomi sun raba Naira tiriliyan 1.92 a watan Nuwamba

A baya, mun wallafa cewa Sanatan Osun ta Gabas, Francis Fadahunsi, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a bangaren tsaron Najeriya.

Sanatan ya ce daga cikin muhimman gyaran da ya kamata a yi akwai nada tsohon soja a matsayin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro na Kasa (NSA) domin a samu abin da ake so.

Wannan kira na Fadahunsi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin labarai, Sam Segun-Progress, ya fitar, inda ya ce yanayin rashin tsaron na kara tabarbarewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng