Abba Hikima, Ɗan Bello Sun Tsayawa Ƴan N Power a Kotu, Ana Shirin Ƙwato Masu Hakkinsu

Abba Hikima, Ɗan Bello Sun Tsayawa Ƴan N Power a Kotu, Ana Shirin Ƙwato Masu Hakkinsu

  • An samu ci gaba a shari’ar N-Power da masu fafutukar kare hakkin 'dan adam, Barista Abba Hikima da Dan Bello suka shigar a Kotun Kwadago ta Ƙasa
  • Kotun ta sanya ranar 15 ga Janairu, 2026 domin ambaton shari’ar a Abuja bayan su Dr. Bello Galadanchi sun nemi a biya matasa hakkokinsu
  • Jama’a sun yaba da rawar da Dan Bello da Barrista Abba Hikima ke takawa wajen kwato masu 'yanci, har ma sun ce akwai wani shiri da kudi suka makale

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – An samu gagarumin ci gaba a shari’ar N-Power da Dr. Bello Galadanchi da aka fi sani da Dan Bello da sauran masu ruwa da tsaki suka shigar a gaban Kotun Kwadago ta Ƙasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Shugaban Majalisa, Akpabio ya ambato masu hana Najeriya zaman lafiya

Barista Abba Hikima, fitaccen lauya a Kano da Dan Bello ne sulka jagoranci shigar da ƙarar a kan Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci ta Tarayya.

An fara samun ci gaba a shari'ar da su Abba Hikima suka shigar
Dan Bello tare da Abba Hikima (H), Dan Bello shi kadai (D) Hoto: Dan Bello
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin sakon da Dan Bello ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya tabbatar da cewa yanzu kotu ta fara daukan mataki a kan korafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu za ta fara shari'ar N-power

Baya ga Ma'aikatar jin kai, masu fafutukar na zargin wasu hukumomi da rashin biyan albashi da alawus-alawus na N-Power da aka dade ana bin gwamnati.

A sabon matakin da aka dauka, kotun ta sanya ranar 15 ga Janairu, 2026, da 9.00 na safe domin ambaton shari’ar.

Za a gudanar da zaman ne a harabar kotun da ke Port-Harcourt Crescent, Area 11, Garki, Abuja. Wannan ci gaba ya nuna cewa shari’ar na tafiya bisa tsarin doka, ba tare da tangarda ba.

Dan Bello ya jinjinawa Abba Hikima
Fitaccen lauya mai kare hakkin jama'a, Abba Hikima Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Masu shigar da ƙarar sun bayyana cewa wannan mataki ya ƙara musu ƙwarin gwiwa, musamman ga dubban matasan N-Power da suka shafe lokaci mai tsawo suna jiran hakkokinsu.

Sun jaddada cewa manufarsu ita ce a samu adalci cikin lumana, tare da tabbatar da cewa an biya duk wani albashi ko alawus da ya tsaya.

Kara karanta wannan

"A bar shi ya huta": Nasir El Rufa'i ya yi magana game da littafi kan Buhari

Haka kuma, Dan Bello ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Barrister Abba Hikima girma da daukaka bisa jajircewarsa a wannan tafarki.

Ra’ayoyin jama’a kan shari'ar N-power

Bayan fitar da bayanin ci gaban shari’ar, jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu tare da yaba wa masu fafutukar.

Dan Bello Uzaifa Danjuma ya ce:

"Muna godiya Abba Hikima da Dan Bello koda a ce ba ayi nasara a karan da aka shigar ba, mun san wannan ci gaba ne kuma mun san an yi yunkuri shari'a da gwamnati wanda a baya mutane da yawa suna ga ba a iya shari'a da gwamnati. Muna godiya sosai da wayar wa al'umma kai da ku ke yi"

Sadees Muhammad J Ladi ya ce:

"Akwai 'Yan batch A da B ne an ba su horo bayan kammalawa kuma gwamnati ta bayar da shaidar horo ta fitar da makudan kudi na jari domin dogaro da kai, amma aka ce su jira, har yau shiru. Su ma a shigar da kararsu."

'Dan Bello ya magantu kan gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

Kotu ta shirya, za ta zartar da hukuncin a kan Abba Kyari da 'yan uwansa

A wani labarin, kun ji cewa Bello Habib Galadanchi, wanda aka fi sani da Dan Bello, ya sake fito wa fili yana caccakar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da zarginta da sa mutane a wahala.

Matashin 'dan gwagwarmayar ya zargi manufofin gwamnatin Najeriya da jefa talakawa a cikin matsanancin hali na yunwa da talauci, baya ga ga sauran matsalolin da ake fama da su.

Ya ce idan har bidiyoyinsa da kalamansa na damun masu mulki, hakan na nuna cewa saƙon da yake isarwa yana isa ga jama’a, domin akwai bukatar a gyara halin da kasar nan ke ciki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng