Ta'addanci: Shugaban Majalisa, Akpabio Ya Ambato Masu Hana Najeriya Zaman Lafiya
- Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya ce wasu sun shirya rura wutar rashin tsaro a Najeriya domin azabtar da kasa baki daya
- Yana wannan batu ne a yayin da ake samun karuwar tashe-tashen hankula a wasu jihohi da ke Arewacin Najeriya inda 'yan ta'adda ke sha'aninsu
- Akpabio ya bayyana mutanen da ke cin moriyar rashin tsaron tare da nuna godiya ga matsayar Shugaban Kasa a kan magance matsalar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana damuwa matuƙa kan abin da ya kira shiryayyen rashin tsaro a Najeriya.
Ya bayyana cewa wasu makiya marasa kishi suna suna ƙoƙarin gallaza wa Najeriya ta hanyar ta’addanci, fashi da makami da tayar da ƙayar baya.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Akpabio ya yi wannan jawabi ne a taron jam’iyyar APC karo na 14 da aka gudanar a dakin taro na State House Conference Centre, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya yi magana game da rashin tsaro
Daily Post ta wallafa cewa Akpabio ya bayyana cewa yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara ya jefa jihohi da dama cikin jimami, inda iyalai ke rasa ‘yan uwansu.
A cewarsa, yayin da jam’iyyar ke ƙara girma, dole ne a fuskanci hassada da ƙiyayya, waɗanda ke haifar da ƙalubale masu tsanani.

Source: Facebook
Ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin jam’iyyar cewa APC na tare da shi tare da addu’a domin ya shawo kan matsalolin tsaron da ƙasar ke ciki.
Akpabio ya ce kwamitin APC na taya jihohin da ke jimamin asarar rayuka sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga takaici wadannan munanan lamura.
Akpabio ya yabi Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan
'Buhari ya yi zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye a Aso Rock
Sanata Godswill Akpabio ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu bisa nasarar ceto sama da yara 100 da aka sace kwanan nan, tare da roƙon Allah ya ba shi ikon ceto sauran yaran domin su koma hannun iyalansu.
Haka kuma, ya jajanta wa iyalan jami’an tsaro da fararen hula da suka rasa rayukansu yayin kare jama’a da dukiyoyi, inda ya jadda da cewa zaman lafiyar kasar nan na da alaka da makwabtanta.
Shugaban Majalisar Dattawan ya yabawa Shugaba Tinubu bisa shiga tsakani a Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuraɗiyya. Ya bukaci a ci gaba da irin wannan haɗin gwiwa a yankin.
Akpabio ya bayyana cewa Majalisar Dattawa ta dauki manyan matakai domin dakile aikata laifuffuka, ciki har da ƙoƙarin sanya laifin satar mutane a matsayin ta’addanci, wanda zai iya kai wa hukuncin kisa.
Yayin da ake jiran Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan dokar, Akpabio ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi da su aiwatar da dokokin laifuffukan da ke da hukuncin kisa, yana mai cewa jinkiri na iya ƙarfafa masu laifi.
An ji gaskiyar rashin lafiyan Akpabio
A wani labarin, kun ji cewa Mashawarcin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan harkokin sadarwa, Kenny Okolugbo, ya yi magana game da rade-radinrashin lafiyan Sanatan.
Kenny Okolugbo ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta game da cewa ubangidansa na fama da rashin lafiya, inda aka ce Akpabio ya yanke jiki ya fadi.
Mista Okolugbo ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin jita-jitar, yana mai jaddada cewa Shugaban Majalisar Dattawan na cikin ƙoshin lafiya, saboda haka a watsar da batun baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

