‘Ya Kamata a Rataye Shi’: Sanata Oshiomhole Ya Ji Daɗin Cire Farouk daga NMDPRA
- Sanata Adams Oshiomhole ya ce ya yi murnar murabus din shugabannin NMDPRA da NUPRC daga mukamansu
- Oshiomhole ya ce ya ji dadi ne saboda haka ya zama dole domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga rugujewa
- Sanata David Jimkuta ya goyi bayan sanatan yayin tantance sababbin shugabannin hukumomin da Bola Tinubu ya tura
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa ya yi murnar murabus din shugabannin NMDPRA da NUPRC.
Oshiomhole ya ce ficewar Injiniya Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe daga mukamansu ya zama dole domin ceton tattalin arzikin Najeriya gaba daya.

Source: Twitter
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin tantance mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya nada shugabannin hukumar NUPRC da NMDPRA, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da Dangote ke yi kan Farouk
Nadin ya biyo bayan murabus din Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe, wadanda aka nada a 2021 karkashin dokar man fetur.
Sauyin ya biyo bayan rikici tsakanin Farouk Ahmed da shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, kan batun shigo da man fetur.
Dangote ya zargi NMDPRA da hana matatun mai na gida ci gaba ta hanyar bayar da lasisin shigo da man fetur daga waje.
Shugaba Tinubu ya mika sunan Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin shugaban NUPRC, da Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban NMDPRA.

Source: Facebook
Sanata Oshiomhole ya dura kan Farouk Ahmed
A yayin tantancewar, Oshiomhole ya soki abin da ya kira manufofi marasa kan gado da tsohon shugaban ya aiwatar.
“Ina murna da aka cire su, har jiya ma da dare na yi murna, ya kamata a rataye shi, a magana ta a baya na ce idan ba a rataye shi ba, zai rataye Najeriya.
"Saboda duk wanda ke adawa da samar da ayyuka a Najeriya, ya zabi shigo da talauci Najeriya amma yake kai arzikinmu waje, bai kamata ya rayu ba."
Ya ce matsalar ba cancanta ba ce, illa dai manufofin da suka gurgunta masana’antu da kuma damar samar da ayyukan yi.
Sanatan Taraba ta Kudu, David Jimkuta, ya goyi bayan Oshiomhole yayin zaman Majalisar Dattawa, inda ya ce zai mara masa baya wajen tambayoyi ga sababbin shugabannin.
Yadda ake zargin Farouk da ruguza kasa
A cewarsa, Oshiomhole ya ce tsofaffin shugabannin sun fifita shigo da mai daga waje maimakon bunkasa matatun mai na cikin gida.
“Duk wanda baya son a samar da aiki a Najeriya, bai dace ya rike wannan bangare ba."
- In ji Oshiomhole.
Ya bukaci sababbin nadin su rika bin muradun kasa maimakon saukin kasuwanci ko ribar wasu ‘yan tsiraru, cewar Premium Times.
NMDPRA: An maka Tinubu a kotu
Mun ba ku labarin cewa wata kungiya ta shigar da kara a kotu kan zargin rashin gaskiya da ake yi wa tsohon Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed.
Karar ta biyo bayan zargin da Aliko Dangote na cewa Farouk Ahmed na aikata almundahana da cin mutuncin kujerarsa.
Kungiyar na neman a yi bincike, a dakatar, tare da gurfanar da tsohon Shugaban NMDPRA a gaban kotu domin gaskiya ta yi halinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


