Majalisa Ta Ɗauki Mataki kan Wani Mamba da Aka Gano Ya Naɗi Sautin Zaman Sirri
- Majalisar dokokin jihar Kwara ta dakatar da Hon. Saba Gideon na tsawon watanni uku kan zargin raina majalisa da karya wasu dokoki
- An rahoto cewa dan majalisar ya amince ya nadi sauti a taron sirri na majalisa sannan ya tura sautin ga wani wanda ba dan majalisa ba
- Majalisar Kwara ta umurce shi da ya rubuta wasikar neman afuwa cikin wa’adin dakatarwarsa, yayin da hukuncin ya fara aiki nan take
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Majalisar dokokin jihar Kwara ta dauki matakin dakatar da Hon. Saba Gideon, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Edu, na tsawon watanni uku.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan an zarge shi da aikata laifuffukan da suka shafi raina majalisa da karya dokokin kare sirrin ayyukanta.

Source: Facebook
'Dan majalisa ya nadi sautin zaman majalisa
An bayyana cewa Hon. Gideon ya nadi wani taron sirri na majalisar ba tare da izini ba, sannan ya yada sautin ga wani mutum da ba shi da hurumin samun irin wadannan bayanai, a cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa wannan abu da dan majalisar ya aikata ya janyo ce-ce-ku-ce a majalisar tare da tada muhawara kan mutunta dokoki da ka’idojin majalisa.
A zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis, ‘yan majalisar Kwara sun bayyana cewa an gano lamarin ne bayan samun bayanai cewa an fitar da sautin taron sirri zuwa waje.
Lokacin da aka kawo batun gaban majalisa, an ce Hon. Saba Gideon ya amince da aikata laifin ba tare da wata doguwar jayayya ba.
An gabatar da bukatar dakatar da 'dan majalisar
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Abdulkadir Magaji, ne ya gabatar da kudurin dakatar da Hon. Sava Gideon ba tare da sanarwa ba.
Abdulkadir Magaji ya kare kudurinsa da Sashe na 4, Doka ta 14 na dokokin majalisar kan gata, da kuma Sashe na 14(2) na Dokar Ikon Majalisun Dokoki ta shekarar 2017.
Wasu ‘yan majalisa da suka tofa albarkacin bakinsu a kan wannan kudi, har ma suka nuna muhimmancin daukar matakin sun hada da Ganiyu Salaudeen (Omupo) da Musa Kareem (Patigi).
Sauran 'yan majalisar sun hada da Owolabi Rasaq (Shaare/Oke-Ode), Abdullahi Danbaba (Kaiama/Kemanji/Wajibe) da kuma Oniboki Yunusa (Afon).

Source: Original
Majalisa ta dakatar da wakilin mazabar Edu
Wadannan 'yan majalisar sun bayyana cewa daukar matakin dakatar da Hon. Gideon ya zama dole domin kare mutuncin majalisa, in ji rahoton Vanguard.
Da yake karanta kudurin majalisar, shugaban majalisar dokokin Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, ya ce abin da dan majalisar ya aikata na iya jefa majalisar cikin abin kunya da rage martabarta a idon jama’a.
Majalisar ta yanke shawarar dakatar da Hon. Saba Gideon na tsawon watanni uku, tare da umartar sa da ya rubuta wasikar neman afuwa a cikin wa’adin dakatarwar. An kuma tabbatar da cewa hukuncin ya fara aiki nan take.
Kwara: Yakubu ya zama shugaban majalisa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar dokokin jihar Kwara ta sake zaɓar matashi mai shekara 38 a matsayin saɓon wanda zai jagorance ta.
Injiniya Yakubu Danladi-Salihu, mai wakiltar mazaɓar, Ilesa/Gwanara a ƙaramar hukumar Baruten ta jihar shi ne ya lashe zaben zama kakakin majalisar ta 10.
An sake zaɓen Yakubu a matsayin kakakin majalisar karo na biyu bayan kuɗirin da Hon Halidu Danbaba ya gabatar wanda Hon Fatimah Lawal ta goyi baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


