Tinubu Ya Cire Sunan Ramat, Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NERC
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake nada sabon kwamitin hukumar kula da wutar lantarki ta Najeria, NERC
- Hakan ya biyo bayan Majalisar Dattawa ta amince da mambobinsa domin karfafa bangaren wutar lantarki a kasar
- Tinubu ya bukaci kwamitin NERC ya kara zurfafa gyaran bangaren wuta bisa dokar wuta ta shekarar 2023
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake kafa kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC.
Tinubu ya dauki wannan mataki ne bayan tantancewar da aka yi musu daga Majalisar Dattawa domin ci gaba da kawo sauyi a bangaren wuta.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi zanga-zanga kan Ramat a Abuja
Hakan na zuwa bayan rasa sunan Abdullahi Ramat wanda ke rike da kujerar a baya kafin ba Olalekan Oseni a baya.
Lamarin ya jawo ta da jijiyoyin wuya a jihar Kano da ma wasu sassan Najeriya da aka yi zanga-zanga a Abuja.
Wasu masu zanga-zanga sun nuna damuwa da cewa sun gaji da jira game da tantance shi inda suka dira majalisar dattawa don nuna fushinsu kan jinkirin.
Masu zanga-zangar sun sanar da majalisar illar rashin tabbatar da Ramat a shugabancin hukumar NERC.

Source: Facebook
Sabon shugaban kwamitin gudanarwa na NERC
Majalisar Dattawa ta amince da mambobin kwamitin ne a ranar 16 ga Disamba, 2025, kamar yadda dokar wutar lantarki ta tanadar ta shekarar 2023.
An nada Dr Mulisiu Olalekan Oseni, wanda ya fara aiki a NERC tun shekarar 2017 a matsayin shugaban kwamitin daga ranar 1 ga Disamba, 2025.
Nadin Oseni zai ci gaba har zuwa lokacin da zai kammala wa’adinsa na shekaru 10 a hukumar, bisa tanadin dokar wutar lantarki ta kasa.
Dr Yusuf Ali, wanda aka fara nada shi kwamishina a 2022, ya zama mataimakin shugaban kwamitin daga 1 ga Disamba, 2025.
Sauran mambobin kwamitin gudanawarwar NERC
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Nathan Rogers Shatti, Dafe Akpeneye, Aisha Mahmud Kanti Bello, Dr Chidi Ike da Dr Fouad Animashaun.
Dr Fouad Animashaun kwararre ne a fannin attalin arzikin makamashi, kuma ya taba rike mukamin shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta jihar Lagos.
Shugaba Tinubu ya bukaci kwamitin NERC ya kara zurfafa sauye-sauyen bangaren wutar lantarki, tare da bin dokar wuta ta shekarar 2023 dalla-dalla.
Yadda Ramat ya rasa kujerarsa a NERC
A baya, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin Shugabannin NERC, amma babu sunan Abdullahi Ramat daga jihar Kano.
A baya, Majalisar Dattawan ta ce Injiniya Ramat, ya gamu da cikas bayan rikice-rikicen siyasa da koke-koken jama’a a kansa, wanda ya sa dole aka dakata daga maganar tantancewar.
Rahotanni sun nuna rikicin siyasar Kano ya taka rawa wajen hana tabbatar da shi, yayin da gwamnati ke duba Dr. Oseni a matsayin sabon shugaban hukumar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


