Gwamna Uba Sani Ya Jero Wasu Manyan Dalilai 4 da Ke Rura Wutar Ta'addanci a Arewa
- Gwamna Uba Sani ya ce talauci, wariya, da wasu manyan matsaloli biyu ne musabbabin rashin tsaro a Arewa maso Yamma
- Ya buƙaci haɗin gwiwar jihohi, musayar bayanan sirri da tsare-tsaren tsaro na bai ɗaya domin magance matsalolin tsaro a shiyyar
- Sarkin Musulmi da ministan tsaro sun jaddada cewa samar da tsaro na buƙatar haɗin kai da dabarun da ba sa bukatar amfani da ƙarfi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya jero wasu manyan matsaloli hudu da yake ganin su ne ke rura wutar ta'addanci a shiyyar Arewa.
A cewar Uba Sani, talauci, wariya, yaɗa bayanan ƙarya da rashin haɗin kai a tsakanin al’umma ne ke tsananta matsalar rashin tsaro, musamman a Arewa maso Yamma.

Source: Twitter
Gwamna Uba Sani ya yi magana kan tsaro
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron koli na zaman lafiya da tsaro na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna a ranar Laraba, in ji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Uba Sani, wanda Sule Shaibu, SAN, kwamishinan harkokin tsaro da harkokin cikin gida ya wakilta, ya ce babu wata jiha ko hukuma guda da za ta iya magance rashin tsaro ita kaɗai.
Ya jaddada muhimmancin musayar bayanan sirri, ayyukan tsaro na bai ɗaya da haɗin gwiwar jihohi, ganin yadda matsalolin tsaro ke ketare iyakokin jihohi.
Tsarin shirin zaman lafiya a jihar Kaduna
Ya ambaci nasarar shirin zaman lafiya na Kaduna (KPM), wanda ya ce tsari ne na tsaro da ke mayar da hankali kan jama’a, bayanan sirri da hanyoyin sulhu ba tare da amfani da makami ba.
A cewarsa, tsarin KPM ya na shafar ba da tallafin kayan aiki ga jami’an tsaro, da tattaunawa, sasanci, ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da adalci, in ji rahoton Business Day.
Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatin Kaduna na aiwatar da ayyukan da suka shafi kowa, ta hanyar faɗaɗa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da tallafin jin ƙai ga matasa da mata.

Source: Facebook
Sarki da ministan tsaro sun yi magana
A nasa jawabin, Sarkin Musulmai, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce ba za a samu ci gaba ba a inda babu tsaro, yana kira ga haɗin gwiwa domin shawo kan matsalolin.
Sarkin, wanda Muhammadu Isa Muhammadu II, sarkin Jama’a, ya wakilta, ya bukaci shugabannin addinai su inganta tattaunawar addinai da koyar da tausayi, yafiya da zaman tare.
Haka nan, ministan tsaro, Christopher Musa, wanda Hussain Kasim, mai ba shi shawara na musamman, ya wakilta, ya ce ba amfani da ƙarfi kaɗai zai kawo ƙarshen rashin tsaro ba.
Uba Sani ya nuna damuwa kan matsalar tsaro
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin Arewa maso Yamma.
Gwamna Uba Sani ya ce iyakokin kasar nan da ke a bude da yawaitar fataucin miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke hura wutar rashin tsaro a yankin.
Ya ce masu fataucin miyagun kwayoyi da masu safarar kayayyaki na tsallake iyaka cikin sauki sosai, sannan idan an matsa musu, suna guduwa zuwa kasashe makwabta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


