Gwamnatin Tarayya Ta Bude Makarantu 47 da Aka Rufe a Fadin Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Bude Makarantu 47 da Aka Rufe a Fadin Najeriya

  • Ma'aikatar ilimi ta tarayyya ta tabbatar da bude duka makarantun sakandire na gwamnatin tarayya 47 da aka rufe a kwanakin baya
  • Tun farko gwamnati ta rufe wadannan makarantu ne saboda tabarbarewa tsaro bayan sace dalibai da malamai a Kebbi da Neja
  • Ma'aikatar ilimi ta ce a yanzu tsaro ya inganta a makarantun da kewaye, kuma dalibai sun koma karatu, wasu sun gama jarabawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya - Gwamnatin tarayya ta sanar da sake bude makarantun sakandire 47 da ta rufe sakamakon tabarbarewar matsalar tsaro a wasu sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Labarin tsohon sakataren Buhari da ministoci da mukarraban gwamnati ke shakka

Idan baku manta ba, gwamnatin ta rufe makarantun ne biyo bayan hare-haren da 'yan bindiga suka kai tare da sace dalibai da malamai a jihohin Kebbi da Neja.

Tunji Alausa.
Ministan ilimi na Najeriya, Dr. Tunji Alausa Hoto: @TunjiAlausa
Source: Facebook

Sai dai a yau Alhamis, 18 ga watan Disamba, 2025, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da bude duka wadannan makarantu guda 47, in ji rahoton Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, inda ta jaddada ƙudurin gwamnati na kare ɗalibai tare da tabbatar da ci gaba da karatu ba tare da tangarda ba.

Dalibai sun koma karatu

Sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta sanya wa hannu, ta ce an ƙarfafa tsaro a cikin makarantum da kewayen su.

Ya ce bayan tabbatar da tsaro ya inganta, dalibai da malamai sun koma sun ci gaba da harkokin karatu yadda ya kamata

A rahoton Daily Trust, sanarwar ta ce:

“Bayan an ƙarfafa tsarin tsaro a makarantu da kewayen su, harkokin karatu sun koma yadda ya kamata. Dalibai sun koma makarantu lafiya, inda da dama daga cikinsu ke shirye-shiryen karisa zangon karatu a watan Disamba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Abba ya dauki sabon mataki don kare rayuka a Kano

"Wasu makarantun kuma sun riga sun kammala jarabawarsu cikin nasara."

Matakan da gwamnatin tarayya ta dauka

Ma’aikatar ilimi ta tabbatar wa iyaye, masu kula da yara da kuma al’umma gaba ɗaya cewa lafiyar ɗalibai, walwalarsu da jin daɗinsu na daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci.

Ta ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da dawo da daidaito a dukkan makarantu a fadin ƙasar.

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu a fadarsa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa dawowar ɗalibai lafiya da nasarar gudanar da jarabawa a makarantu da dama na nuna ƙudurin gwamnati na tabbatar da cewa karatu bai tsaya ba duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

An rufe makarantu a jihar Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta dauki matakin rufe makarantu biyo bayan harin da 'yan bindiga suka kai inda suka sace dalibai.

Hakan na cikin wata sanarwar hadimin gwiwada kwamishinan ilmin manyan makarantu, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, da kwamishinar ilmin firamare da sakandare, Dr. Halima Bande, suka fitar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gobara ta babbake gidan tsohon gwamnan Zamfara, an tafka asara

Sanarwar ta ce rufe makarantun na da nasaba da hare-haren da ’yan bindiga suka kai a wasu yankuna na jihar kwa nan nan, lamarin da ya sanya ya zama dole a dauki matakin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262