Abin Boye Ya Fito: 'Yar Buhari Ta Fadi yadda Ake Amfani da Sa Hannun Marigayin
- Fatima Buhari ta ce an gano takardun gwamnati da ke dauke da sa hannun bogi na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari
- Ta ce wasu jawabai da umarnin Buhari ana sauya su bayan ya amince da su, lamarin da ke nuna tasirin wasu a cikin gwamnati
- Littafin tarihin marigayi Buhari ya bayyana cewa tsohon shugaban ya yi zargin ana leken asiri a ofishinsa a Aso Rock Villa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - 'Yar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta yi karin haske kan zargin amfani da sa hannun marigayin na bogi.
Fatima Buhari ta bayyana cewa a lokacin mulkin mahaifinta, an yi ta kirkirar sa hannunsa a wasu takardun gwamnati.

Source: Twitter
Fatima ta bankado abubuwa a mulkin Buhari
Fatima ta bayyana hakan ne a cikin littafin From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari, wanda marubuci Charles Omole ya wallafa, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce ita kwararriyar mai bincike ce, kuma ta duba wasu muhimman takardu inda ta gano sa hannun bogi da aka jingina wa mahaifinta, sannan ta nuna masa hujjojin da idonta ya gani.
A cewar littafin, ba ita kadai ba ce ta yi wannan zargi, domin wasu mutane ma sun taba nuna damuwa kan yiwuwar kirkirar sa hannunsa a lokacin.
Sai dai Fatima ta jaddada cewa wannan matsala ba ta takaita ga mulkin Buhari kadai ba, inda ta ce irin wannan lamari ya taba faruwa a gwamnatocin baya.
Yadda ake cin dunduniyar shugaba Buhari
Littafin ya kuma bayyana cewa wasu jawaban Buhari da umarninsa ana canza su bayan ya amince da su.
A wani misali, an ce Buhari ya yi jawabi a wani taro a kasar Amurka, inda Fatima ke zaune a dakin taron, cewar Punch.
Ta lura yana tsayawa yana karantawa ba kamar yadda ya saba ba, sannan daga baya ya shaida mata cewa jawabin da ke hannunsa ba shi ne wanda ya amince da shi ba.

Source: Instagram
Yadda ake sauya kalaman Buhari a gwamnati
A cewar littafin, wannan ba sabon abu ba ne, domin ana yawan rage karfin umarni, canza kalamai, ko juya manufar shugaba yayin da takardu ke wucewa daga ofis zuwa ofis a cikin manyan ma’aikatun gwamnati.
Littafin ya ce wasu lokuta kuskure ne na tsarin aiki, amma a wasu lokutan aikin wasu ne da ke da iko a ciki.
Haka kuma, littafin ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari ya yi imanin ana leken asiri a ofishinsa da ke Aso Villa.
An ce wasu lokuta yana guje wa magana kai tsaye da ‘yarsa, yana amfani da alamomi ko rubuce-rubuce, saboda tsoron ana sauraron hirarrakinsu.
'Ku bar Buhari ya huta' - El-Rufai
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shiga maganar sabon lttafi kan Muhammadu Buhari da aka kaddamar.
El-Rufai ya bukaci a bar marigayi marigayin ya huta bayan rasuwarsa ba tare da maganganu a kansa ba.
Ya nuna damuwa kan yadda ake kokarin sake fassara tarihin Buhari domin cimma bukatunsu na siyasa maimaikon koyi fa shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


