Ba a Gama Murnar Cin Zabe ba, Yan Ta'adda Sun Sace Mataimakin Ciyaman da Kansiloli 2
- Mayakan Boko Haram/ISWAP sun yi garkuwa da zababben mataimakin shugaban karamar hukumar Biu, Alhaji Saidu a jihar Borno
- 'Dan siyasar yana daya daga cikin wadanda suka samu nasara a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a Borno ranar Asabar da ta wuce
- 'Yan ta'addan sun kuma sace wasu kansiloli biyu da matafiya da dama a harin da suka kai ranar Laraba a kan titin Biu zuwa Maiduguri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - ’Yan ta’adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram/ISWAP ne sun yi garkuwa da sabon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Biu da kansiloli biyu a Jihar Borno
Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’adda sun sace mutanen ne kwanaki kadan bayan zaben kananan hukumomin Borno, wanda aka gudanar ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025.

Source: Original
Vanguard ta tattaro cewa wadanda 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su sun hada da Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Biu, Alhaji Saidu, tare da kansiloli biyu da ke wakiltar mazabun Zarawuyaku da Miringa, a Jihar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka sace matafiya a Borno
An ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Laraba a tsakanin ƙauyen Kamuya da hanyar Buni Yadi, yayin da mutanen ke kan hanyarsu daga Biu zuwa Maiduguri, babban birnin jihar.
Haka kuma, wasu fasinjoji da ba a tantance su ba, waɗanda ke tafiya a cikin wata motar Hizbah daga garin Potiskum na Jihar Yobe zuwa Biu, suma sun fada hannun masu garkuwa da mutanen.
Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa ɗaya daga cikin kansilolin da aka sace shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Biu da ya gabata, cewar rahoton Daily Post.
'Dan siyasa ya roki jami'an tsaro
Wani babban ɗan siyasa a yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce:
“Eh, sabon zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Biu, Alhaji Saidu, da kansiloli biyu masu wakiltar Zarawuyaku da Miringa, sun fada hannun ’yan Boko Haram/ISWAP a tsakanin Kamuya da hanyar Buni Yadi.
“An sace su ne tare da wasu fasinjoji da ke tafiya a motar Hizbah daga Potiskum zuwa Biu. Muna roƙon gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse domin ceto su da sauran mutanen da ke hannun ’yan ta’adda lafiya.”

Source: Twitter
Titin Biu–Buratai–Kamuya–Buni–Damaturu mai tsawon kusan kilomita 120 ya shahara wajen zama hadari ga matafiya saboda yawan hare-haren yan ta'adda.
Sojoji sun yi kuskuren jefa bam a Borno
A wani rahoton, kun ji cewa jiragen yaki na Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) sun yi kuskuren jefa bama-bamai kan fararen hula a jihar Borno.
An kashe fararen hular ne a yayin wani hari da sojojin saman suka kai kan wuraren da ake zargin ’yan ta’adda ke amfani da su a jihar Borno a ranar Lahadi da ta gabata.
Rahotanni sun ce sojojin sun saki ruwan bama bamai kan masunta da direbobin motocin haya da suka taru a tsakanin Daban Masara a Kukawa da Badeiri a karamar hukumar Marte.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

