An Harbe Dan Kwallon Barcelona SC, Mario Pineida, Ya Mutu Nan Take
- ’Yan sandan Ecuador sun tabbatar da mutuwar ɗan wasan kasa da kasa, Mario Pineida bayan wani hari da aka kai masa a birnin Guayaquil
- Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙaruwar rikice-rikicen tsaro da hare-haren ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka a ƙasar
- Rahoto ya nuna cewa kungiyarsa ta Barcelona SC da ma’aikatar cikin gida na kasar Ecuador sun nuna alhini a dalilin rasuwar ɗan wasan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ecuador – Dan wasan ƙwallon ƙafa na Ecuador, Mario Pineida, ya rasu bayan an harbe shi a wani hari da aka kai a birnin Guayaquil, kamar yadda ’yan sandan ƙasar suka tabbatar.
Mario Pineida, mai shekaru 33, ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona SC tare da wakiltar ƙasarsa a lokuta da dama.

Kara karanta wannan
Tattaunawar Buhari da Lai Mohammed a kan toshe amfani da Twitter a Najeriya a 2021

Source: Getty Images
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona SC ta sanar da rasuwar dan wasan a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar ’yan sandan kasar Ecuador, wani mutum guda ma ya mutu a harin, yayin da wani na uku ya jikkata sosai.
Rahoton BBC ya nuna cewa an kashe Pineida ne a ranar Laraba yayin wani harbi a yankin Samanes da ke arewacin Guayaquil.
Bayani kan harbin Mario Pineida
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Ecuador ta tabbatar da mutuwar Pineida, amma ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba.
Sai dai duk da haka, wasu kafafen watsa labarai na cikin gida sun ce wasu mutane biyu da ke kan babura ne suka kai harin.
Rahoton Al-Jazeera ya ce maharan sun buɗe wuta kan Pineida tare da wasu mata biyu da suka haɗa da mahaifiyarsa.
Wannan lamari ya ƙara tayar da hankula a birnin da ke fama da hare-haren ƙungiyoyin daba da masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Tarihin Mario Pineida a ƙwallon ƙafa
Mario Pineida ya fara ƙwallon ƙafa a kulob din Independiente del Valle daga 2010 zuwa 2015. Daga nan ya koma Barcelona SC a 2016, inda ya lashe kofi sau biyu.
Ya kuma samu ɗan gajeren zama a kulob din Fluminense na Brazil a 2022, kafin daga bisani ya ci gaba da taka leda a cikin gida.
A matakin ƙasa, Pineida ya buga wasanni takwas yana wakiltar Ecuador, ciki har da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.
Rawar da Pineida ya taka a ƙasar Ecuador
Kodayake bai shiga cikin tawagar da ta samu shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 ba, Pineida ya kasance cikin jerin ’yan wasan da suka wakilci Ecuador a manyan wasanni.
Wasansa na ƙarshe a tawagar ƙasa ya kasance a gasar Copa America ta 2021, inda ya taka leda a wasan rukuni da suka buga da Brazil.

Source: Getty Images
Haka kuma, marigayin ya halarci gasar Copa America ta 2017, abin da ya ƙara masa kima a tarihin ƙwallon ƙafa na ƙasar.
Ahmed Musa ya yi ritaya a Super Eagles
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan kwallon kafan Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga taka leda a Super Eagles.
'Dan wasan na Kano Pillars ya sanar da haka ne ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2025 a wata sanarwa da ya fitar da kansa.
Ahmed Musa ya bayyana nasarorin da ya samu a kwallon kafa, ciki har da cin kwallaye da dama a gasar kofin duniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

