Tattaunawar Buhari da Lai Mohammed a kan Toshe Amfani da Twitter a Najeriya a 2021
- Tsohon ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya ce dakatar da amfani da Twitter (X) a 2021 na ɗaya daga cikin matakai mafi nauyi da ya taɓa yanke wa
- Ya bayyana cewa tsaron ƙasa ne ya rinjayi duk wata illa da matakin zai iya haifarwa ga ’yan kasuwa da masu amfani da kafar a Najeriya
- Lai Mohammed ya ce shawarar ba ta da alaƙa da goge sakon tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, sabanin rade-radin da suka bazu a lokacin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon ministan yaɗa labarai, Lai Mohammed, ya bayyana cewa dakatar da dandalin sada zumunta na Twitter, wanda yanzu ake kira X, na daga cikin mafi wahalar shawarar da ya ɗauka a lokacinsa.
Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa mai suna Headlines & Soundbites: Media Moments That Defined An Administration, wanda aka ƙaddamar a Abuja a ranar Laraba.

Source: Facebook
The Cable ta rahoto ya bayyana cewa matakin dakatar da Twitter (X) a Yuni, 2021, ya zo ne bayan dogon nazari da la’akari da tsaron ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta dakatar da Twitter ne a wancan lokacin, tana mai cewa ana amfani da dandalin wajen ayyukan da ka iya barazana ga wanzuwar Najeriya da zaman lafiyarta.
Bayanin Lai Muhammad kan toshe Twitter
A babi na 14 na littafin mai shafi 601, Lai Mohammed ya bayyana dalilai biyu da suka sa dakatar da Twitter ta kasance masa mai wahala.
Ya ce na farko shi ne tasirin da hakan zai yi ga ’yan Najeriya da ke amfani da dandalin wajen tallata hajojinsu ko kuma sana’a.
Na biyu, a cewarsa, shi ne yadda matakin zai bayyana a idon duniya dangane da ’yancin faɗar albarkacin baki a tsarin dimokiraɗiyya.
Duk da haka, Lai Mohammed ya ce babu wani daga cikin waɗannan dalilai da ya fi barazanar tsaron ƙasa muhimmanci.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023
Ya jaddada cewa a harkar mulki, dole ne muradin jama’a ya rinjayi muradin ɗaiɗaikun mutane, musamman idan ana ganin wata kafa na iya zama hanyar tayar da hankali.
Abin da Buhari ya cewa Lai Mohammed
Lai Mohammed ya bayyana cewa kafin aiwatar da dakatarwar, ya tuntubi Shugaba Buhari, wanda ya tambaye shi ko dalilin matakin shi ne goge sakonsa, da kuma ko gwamnati na da ikon aiwatar da dakatarwar.
A bayanin da tsohon ministan ya yi a cikin littafin, ya bayyana cewa bayan amsoshin da ya bayar na cewa ba saboda goge sakon Buhari ba ne, shugaban ƙasa ya amince da shawarar.

Source: UGC
Ya ƙara da cewa dakatarwar ba ta zo kwatsam ba, domin gwamnati ta dade tana gargadin kamfanonin sada zumunta da su hana yaɗa labaran ƙarya, ƙiyayya da tayar da hankali.
A ranar 12, Janairu, 2022, gwamnatin tarayya ta janye dakatarwar da ta ɗauki kwanaki 222, inda aka dawo da amfani da Twitter washegari bayan cimma matsaya da masu dandalin.
Yadda iyalan Buhari ke rayuwa a yanzu
A wani labarin, kun ji cewa Aisha Muhammadu Buhari ta yi hira da manema labarai a karon farko bayan kammala idda da ta yi.
Uwar gidan tsohon shugaban kasar ta bayyana cewa masu harka da Buhari sun musu jaje kuma sun koma harkokinsu na yau da kullum.
A bayanin da ta yi, Aisha Buhari ta ce rayuwa ba za ta taba kasance musu kamar lokacin da marigayin yake tare da su ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

