‘Yan Najeriya sun tafka asarar Naira Biliyan 150 a sakamakon haramta aiki da Twitter
- A watan Yuni ne gwamnatin tarayya ta hana kamfanin Twitter aiki a Najeriya
- NetBlocks sun nuna hakan ya jawo mutane sun tafka maduduwar asarar kudi
- Alkaluman sun ce abin da aka yi asara a watannin biyu ya kai Naira Biliyan 150
Najeriya - Akwai yiwuwar kasuwancin Najeriya ya gamu da asarar fam Dala miliyan 366.88, kusan Naira biliyan 150.46 kenan a kudinmu na gida.
Jaridar Punch ta ce an yi wannan babbar asarar ne a sanadiyyar matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na haramta Twitter a ranar 5 ga watan Yuni, 2021.
Kamar yadda muka samu rahoto a makon nan, NetBlocks ne ya yi amfani da kayan aiki, ya yi lissafin wannan asara da tattalin arzikin Najeriya ya yi.
NetBlocks ya ce a kowace sa’a, sai tattalin arzikin Najeriya ya yi asarar $250, 600 (fiye da Naira miliyan 100), saboda hana amfani da dandalin na Twitter.
Zuwa ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, 2021, an shafe kwanaki 61 ko kuma a ce sa’o’i 1464 da hana mutane aiki da Twitter, hakan ya jawo babbar asara.
Miliyoyin mutane sun saba da Twitter a Najeriya
Kamfanin Statista ya fitar da alkaluman da ke nuna cewa akwai sama da mutane miliyan 33 da ke amfani da kafafen sada zumunta na zamani a kasar nan.
Daga cikin wannan adadi, akwai fiye da 25% da su ke Twitter, wannan mataki da gwamnati ta dauka, ya shafi tsakanin mutum miliyan takwas zuwa tara.
Rahoton ya ce a dalilin hana Twitter aiki mutane da dama suka koma amfani da manhajojin VPN domin su iya cigaba da amfani da dandalin ta bayan fage.
Tarihin fadan gwamnati da Twitter
Idan za a tuna a ranar 4 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta bada sanarwar dakatar da aikin kamfanin sada zumunta da yada bayanan na zamani a Najeriya.
Hukumar sadarwa ta soma toshe kafar hawa wannan shafi ta kowace irin manhaja a washegari.
Tun lokacin aka ji ofishin sakataren gwamnatin kasar Amurka ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye matakin da ta dauka na dakatar da Twittter.
Asali: Legit.ng