NMDPRA: An Maka Tinubu a gaban Kotu game da Rikicin Dangote da Farouk
- Wata kungiya ta shigar da kara a kotu kan zargin rashin gaskiya da ake yi wa tsohon Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed
- Karar ta biyo bayan zargin da Aliko Dangote na cewa Farouk Ahmed na aikata almundahana da cin mutuncin kujerarsa
- Kungiyar na neman a yi bincike, a dakatar, tare da gurfanar da tsohon Shugaban NMDPRA a gaban kotu domin gaskiya ta yi halinta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata kungiya mai suna RAI ta shigar da kara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, tana neman a bincike game da rikicin Aliko Dangote da Farouk Ahmed.
Alhaji Aliko Dangote na zargin Farouk Ahmed, tsohon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Tsakiya da Kasa (NMDPRA), bisa zargin rashin gaskiya da kuma yin amfani da mukaminsa wajen amfanin kansa.

Source: Twitter
Premium Times ta wallafa cewa kungiyar ta shigar da karar ne a ranar Laraba, jim kadan bayan bullar labarin cewa Farouk Ahmed da shugaban Hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe, sun yi murabus daga mukamansu.
Zargin da Dangote ya yi wa Farouk
Rahoton ya bayyana cewa karar ta biyo bayan zarge-zargen da Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanin Dangote, ya yi wa Farouk Ahmed.
Dangote ya zargi Ahmed da lalata tattalin arziki, yana cewa ayyukansa na hana cigaban harkar tace man fetur a cikin gida.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Matatar Dangote, Dangote ya ce shugabancin NMDPRA na hada baki da ‘yan kasuwar ketare da masu shigo da man fetur mara kyau.

Source: Getty Images
Dangote ya kuma zargi Farouk Ahmed da rayuwa fiye da karfin albashinsa, yana mai cewa ‘ya’yansa hudu suna karatu a makarantu masu tsada a Switzerland.
A cewarsa, kudin karatun da kula da su ya kai $7m, abin da ya haifar da tambayoyi kan tushen kudin da ya samo wajen biyan kudin.
A ranar Talata, Dangote ya kai koken hukuma ga ICPC ta hannun lauyansa, Ogwu Onoja, SAN, inda ya bukaci a kama, a bincike, tare da gurfanar da Ahmed.
Kungiyar RAI ta shigar da kara a kotu
A karar da RAI ta shigar, lauyan kungiyar Okere Nnamdi ya bukaci kotu ta ayyana cewa Farouk Ahmed ya aikata laifin karban kudi daga hannun wasu ba bisa ka'ida ba.
Kungiyar ta kuma bukaci kotu ta umarci Shugaba Tinubu da ya dakatar da Farouk Ahmed nan take, tare da tilasta wa hukumomin yaki da rashawa irin su ICPC, EFCC da CCB su gudanar da bincike da kai shi kotu.
RAI ta ce ta shigar da kara ne don kare muradin jama’a, tana jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta cin hanci da rashawa.
Kungiyar ta ce ‘yan Najeriya na ci gaba da shan wahala sakamakon cire tallafin man fetur, wanda ta ce asalin matsalar shi ne cin hanci da rashawa a bangaren mai.
Rikici ya barke tsakanin Dangote da Farouk Ahmed
A baya, mun wallafa cewa shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi zargi mai nauyi kan shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiya da Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed.
Shugaban rukunonin Dangote ya yi zargin jami’in gwamnati da biyan kusan Dala miliyan biyar domin karatun sakandaren ‘ya’yansa hudu a kasar Switzerland, kudin da Dangite ke ganin ya haura abin da ya ke samu.
Dangote ya yi kira ga hukumomi da su gudanar da bincike mai zurfi, tare da tilasta wa Farouk Ahmed ya fito fili ya yi wa ‘yan Najeriya bayani kan yadda aka ce ya iya daukar irin wannan nauyin kudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


