Malami: EFCC Ta kai Samame Gidan da 'Yar Marigayi Buhari ke Zaune

Malami: EFCC Ta kai Samame Gidan da 'Yar Marigayi Buhari ke Zaune

  • EFCC ta kai samame zuwa wani gida da ke da alaƙa da tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, a wani mataki da ya janyo da ya ja hankali
  • An ce ’yar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tana cikin gidan a lokacin da jami’an suka kai samamen, wannan zai ƙara jan hankalin jama’a
  • Matakin ya zo ne yayin da bincike mai zurfi ke ci gaba kan zarge-zargen da suka shafi kuɗi da ayyukan ofishin Malami a lokacin da ya ke ministan shari'a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jami’an hukumar EFCC sun rufe wani gida da ke da alaƙa da tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a daren Laraba.

Hakan na cikin matakin da hukumar ta dauka wajen tsananta bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Abubakar Malami wanda ya yi shekaru takwas yana minista.

Kara karanta wannan

"A bar shi ya huta": Nasir El Rufa'i ya yi magana game da littafi kan Buhari

Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami
Abubakar Malami SAN da EFCC ta kai samame gidansa. Hoto: Abubakar Malami SAN|EFCC Nigeria
Source: Twitter

Rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa motoci da dama na EFCC tare da jami’ai masu ɗauke da makamai ne suka mamaye gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Nana Hadiza Buhari, matar Malami ta uku kuma ’yar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tana wurin a lokacin samamen.

EFCC sun garkame gidan Abubakar Malami

Majiyoyi sun bayyana cewa rufe gidan ya zo ne a lokacin da Malami ke ci gaba da kasancewa a tsare, bisa zarge-zarge masu yawa da suka haɗa da cin hanci da yadda aka sarrafa kuɗin da aka kwato daga dukiyar Abacha.

Masu bincike sun kuma karkata hankalinsu kan wasu asusun banki da mu’amaloli na kuɗi da ake zargin suna da alaƙa da lokacin da Malami ya rike muƙamin Antoni Janar.

Rahotanni sun ce wannan sabon mataki alama ce ta yadda EFCC ke ƙoƙarin zurfafa bincike ba tare da la’akari da matsayin siyasa ko dangantaka ba.

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa na hukumar EFCC ta kai samame ne gidajen Malami da ke Abuja da jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi

Malami ya auri 'yar Buhari a 2022

Abubakar Malami ya yi aiki a matsayin babban lauya na gwamnati daga shekarar 2015 zuwa 2023, inda ya kasance daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Muhammadu Buhari.

A watan Yuli na shekarar 2022, Malami ya auri Nana Hadiza Buhari a wani biki na sirri da aka gudanar a masallacin fadar shugaban Ƙasa da ke Aso Rock, a shekarar ƙarshe ta mulkin Buhari.

Buhari da wasu iyalansa a Abuja
Marigayi Buhari da 'ya'yansa a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Nana Hadiza ita ce ’ya ta uku ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Jami’an EFCC sun tabbatar da cewa an bai wa Malami beli, amma daga bisani an soke bayan zargin rashin cika wasu muhimman sharuɗa da aka gindaya masa.

Matsayar Aisha Buhari kan sake aure

A wani labarin, mun kawo muku cewa matar marigayi Muhammadu Buhari ta yi matsaya kan batun sake aure bayansa.

Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana cewa za ta cigaba da kula da yara da jikokin da marigayin ya bari maimakon sake aure.

Kara karanta wannan

An fara gunaguni bayan mai tsaron Tinubu ya zama Birgediya Janar a soja

Uwargidan tsohon shugaban kasar ta bayyana haka ne a littafin tarihin rayuwar marigayin da aka sake kaddamarwa a Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng