EFCC Ta Cafke Bokaye da Kudin Kasashen Waje na Bogi bayan Damfarar 'Yan Najeriya
- Hukumar nan mai alhakin yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke mutane biyar da ake zargi da damfarar jama’a da sunan tsafi
- Ana zargin mutanen da karbar Naira miliyan 26 daga wata mata tare da amfani da dabarar rufa ido wajen karbe mata 'yan kudinta
- An kwato kudaden kasashen waje na bogi, motoci masu tsada da wayoyi, EFCC na kuma shirin daukar mataki a kansu nan gaba kadan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta sanar da kama wasu mutane biyar da ake zargi da hada kai wajen damfarar jama’a ta hanyar yin karyar tsafi.
Haka kuma EFCC ta gano bokayen na karya tsarkake kudi da kuma bayar da magungunan gargajiya na bogi, inda suke amfani da bukatun mutane wajen karba masu 'yan kudinsu.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa hukumar ta ce mutanen suna yaudarar jama’a ne da alkawarin magance cututtuka da kuma samar da kudi ta hanyar aljanu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hukumar EFCC ta kama bokaye
Jaridar Leadership ta wallafa cewa bayanin kama mutanen na cikin wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Laraba.
Dele Oyewale ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan dogon bincike da tattara bayanan sirri game da ayyukansu.

Source: Twitter
A cewar Oyewale, jami’an EFCC sun kama Akingbola Omotayo, Adeola Funsho Ogunrinde, Yahaya Amodu, Kubratu Babalola Olaitan, da Familola Sunday Olaitan a ranakun 7 da 8 ga Disamba, 2025.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin zagon kasar ta bayyana cewa kamen ya faru ne a wuraren da suke kira haikalinsu a jihohin Osun da Legas.
Jami'an EFCC sun kama 'yan damfara
EFCC ta ce kafin kama su, an shafe lokaci ana sa ido da tattara bayanan sirri kan yadda suke gudanar da ayyukansu na damfara.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi
Wadanda ake zargin suna gabatar da kansu a matsayin masu maganin gargajiya da kuma masu ikon tsafi, inda suke jan hankalin mutane masu bukata ko wadanda ke cikin matsanancin hali.
Sanarwar ta ce ana zargin kungiyar da damfarar wata mata mai suna Halima Sanni, inda suka karbi Naira miliyan 26 daga gare ta bisa alkawarin warware mata matsaloli ta hanyar tsafi.
EFCC ta bayyana cewa a yayin samamen da aka kai, jami’anta sun kwato kudin kasashen waje na bogi da yawansu ya kai Dala miliyan 3.4 da kuma Yuro 280,000.
An ce wadannan kudi ana nuna wa wadanda ake damfara su ne a matsayin kudin da aljanu suka samar, amma sai an “tsarkake” su kafin a yi amfani da su.
A cewar Oyewale, wadanda ake zargin suna amfani da dabarar rufa ido, inda suke shawo kan wadanda abin ya shafa su kawo kudi domin a yi hadaya ta ruhaniya kafin a samu damar kashe kudin.
Baya ga kudin bogi, EFCC ta ce an kuma kwato motoci biyu masu tsada da wayoyin hannu daga hannun wadanda ake zargi, wadanda ake ganin an samu su ne daga kudin da aka damfari jama’a.
Hukumar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu da zarar an kammala bincike, tare da gargadin jama'a kan neman kudi ido rufe.
EFCC ta kama malamar coci
A baya, mun wallafa cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta kama wata malamar coci mai suna Archbishop Angel Oyeghe a birnin Warri da ke jihar Delta, bisa zargin aikata laifuffuka.
Hukumar EFCC na zargin Oyeghe da taka doka ta hanyar aikata laifuffukan da suka shafi cin mutuncin takardun kudin Najeriya da kuma wasu laifuffuka na kudi da dokar kasa ta haramta.
Malamar, wacce ita ce ta kafa cocin Faith Healing Ministry a Warri, ta fada hannun jami’an EFCC ne bayan da wani bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta, abin da ya tayar da kura a tsakanin al’umma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
