"A Bar Shi Ya Huta": Nasir El Rufa'i Ya Yi Magana game da Littafi kan Buhari

"A Bar Shi Ya Huta": Nasir El Rufa'i Ya Yi Magana game da Littafi kan Buhari

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bukaci a bar marigayi Muhammadu Buhari ya huta lafiya ba tare da maganganu a kansa ba
  • Ya nuna damuwa kan yadda ake kokarin sake fassara tarihin Buhari domin cimma bukatunsu na siyasa maimaikon koyi fa shi
  • Ya ce girmama Buhari na gaskiya shi ne bin dabi’unsa, ba anfani da sunansa ba ko kokarin muzanta wasu da kusa da shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su bar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya huta lafiya.

Ya yi gargadi game da kokarin tayar da rikici, rarrabuwar kai ko anfani da tarihinsa don cimma wasu bukatun siyasa da jawo maganganu a tsakanin 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ake ganin ya kamata a daure kusan duka ministocin Buhari a gidan yari

El-Rufa'i na son a daina maganganu a kam Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Nasir El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 17 ga Disamba, 2025, bayan kaddamar da wani littafi kan rayuwar marigayi Muhammadu Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufa'i ya magantu game da littafin Buhari

A rubutun, El-Rufa’i ya ce taron kaddamar da littafi a kan tsohon Shugaban Kasa ya tayar masa da hankali, ganin yadda aka sake nuna tsofaffin rarrabuwar kai da ke kewaye da Buhari tun yana raye.

A cewarsa, abin da ya kamata ya zama taron tunawa da Shugaban a cikin mutunci ya koma wani dandali na fifita wasu bangarori tare da ware wasu da su ma suka kasance kusa da Buhari.

El-Rufa'i ya yi zargin ana amfani da sunan Buhari don cimma wasu bukatun siyasa
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

A cewar El-Rufa’i, yadda aka shirya taron kaddamar da littafin da kuma wadanda suka mamaye wurin sun nuna alamun cewa ana kokarin fito da tarihin Buhari bisa muradin wasu mutane, ba bisa cikakken labarinsa ba.

Kara karanta wannan

Bayan rasuwarsa, Aisha ta fadi kuskuren Buhari cikin mulkinsa na shekara 8

Ya kuma nuna damuwa kan ganin wasu daga cikin mutanen da suka kasance masu tsananin suka ga Buhari a lokacin mulkinsa, amma yanzu suke fito suna yaba masa.

El-Rufa’i ya bayyana irin wadannan yabo a matsayin na bogi, yana cewa wadannan mutane su ne a baya ke danganta kusan dukkannin matsalolin Najeriya da mulkin Buhari.

El-Rufa'i ya soki sababbin masu yabon Buhari

A ra’ayinsa, abin damuwa ne yadda wasu da Buhari bai yarda da su ba, ko bai girmama su ba a rayuwarsa, yanzu suke nuna soyayya da kusanci da shi bayan rasuwarsa.

El-Rufa’i ya ce bai kai ga karanta littafin 'Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari' ba, amma rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai sun nuna an karkata zuwa wani bangare.

Duk da ya amince akwai kalubale a mulkin Buhari, amma ya ce daga kwarewarsa ta aiki tare da tsohon Shugaban, ya san yawancin matsalolin mulkinsa sun samo asali ne daga gazawar wasu na kusa da shi.

El-Rufa’i ya bayyana Buhari a matsayin mutum mai tsananin addini, ladabi, gaskiya da kishin kasa. Ya ce hanya mafi dacewa ta girmama shi ita ce bin dabi’unsa na rikon amana, tawali’u da hidimtawa kasa.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Aisha ta magantu game da kuskuren mulkin Buhari

A baya, mun wallafa cewa tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ta kalli wa’adin shekaru takwas na mulkin mijinta, marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kalaman Aisha Buhari sun fito ne a cikin wani littafi mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dr. Charles Omole ya wallafa, kuma aka kaddamar a Fadar Shugaban Kasa.

A cewar Aisha Buhari, akwai wasu ’yan tsirarun dattawa, ’yan uwa da manyan masu fada a ji da suka kewaye marigayi Buhari, suna amfani da dabara da tasiri domin cimma muradun kansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng