Abin da Ya Sa Mutane Suka Fara Shiga Matsalar Wutar Lantarki a Jihohi 4 a Najeriya
- Kamfanin raba wutar lantarki da ke Ibadan (IBEDC) ya bai wa jama'ar yankunan da ke karkashinsa hakuri kan matsalar karancin wuta da ake fuskanta
- Ya ce hakan ta faru ne sakamakon raguwar kason da kamfanin raba wuta na kasa (TCN) ke turo wa kamfanin, wanda hakan ya sa ake yawan dauke wuta
- IBEDC ya tabbatar wa kwastomi cewa nan ba da jimawa ba za a warware matsalar domin samun wuta sosai a Ibadan, Kwara da jihohi 3
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa an fara samun matsalar yawan daukewar wutar lantarki a jihar Kwara da wasu jihohin Najeriya.
Wannan al'amari ya fara jefa mutanen wadannan jihohi cikin duhun rashin hasken wutar lantarki, wanda ke kawo cikas ga wasu daga cikin harkokin kasuwanci.

Source: Getty Images
Dalilin yawan dauke wutar lantarki
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ibadan (IBEDC) ya bayyana dalilin da ya ake samun yawan katsewar wutar lantarki a Kwara, Oyo, Ogun, Ibadan da Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin IBEDC ya bayyana cewa babban tushen wutar lantarki na kasa ta rage yawan adadin wutar da ake turo wa kamfanin, wanda hakan ya sa ake yawan dauke wuta a wadannan jihohi.
Ya ce babu wadatacciyar wuta daga turken wuta na kasa, wanda hakan ya takaita adadin wutar da ake da ita domin rarrabawa a yankunan da kamfanin ke kula da su.
Kanfanin IBEDC ya ba jama'a hakuri
A cikin wata sanarwa da shugabancin kamfanin IBEDC ya fitar ya nuna nadama kan matsalolin da yawan dauke wutar ya jefa mazauna yankunan da kasuwancinsu.
A rahoton da Leadership ta kawo, sanarwar ta ce:
“IBEDC na ci gaba da tattaunawa da Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) da kuma Hukumar Gudanar da Tsarin Wuta Mai Zaman Kanta ta Najeriya (NISO) domin inganta daidaiton samar da wuta.
“A halin yanzu, ana raba wutar da ake da ita cikin tsari da adalci a kan layukan wuta da turakun sabis, domin tabbatar da adalci da ingantaccen aiki.
“Muna gode wa kwastomominmu bisa hakuri da fahimta, kuma muna tabbatar musu da cewa za mu ci gaba da sanar da su yadda al’amura ke tafiya.”

Source: Twitter
Kamfanin ya kara da cewa zai ci gaba da bai wa kwastomomi bayanai yayin da ake samun ci gaba a kokarin da ake yi na daidaita samar da wutar lantarki a Ibadan, Oyo, Kwara, Ogun da Osun.
Matsala ta tunkaro tashoshin wutar lantarki
A wani rahoton na daban, kun ji cewa Kamfanoni sun fara rage samar da gas ga tashoshin wutar lantarki, lamarin da ke barazanar jefa ‘yan Najeriya cikin duhu a lokacin.bukukuwan karismeti.
Rahotanni sun nuna cewa wasu kamfanonin gas sun fara ragewa ko dakatar da samar da makamashin nasu ga tashoshin wuta, saboda basussukan da ake bin su.
Duk da amincewar gwamnatin tarayya ta yi na biyan bashin masu gas a Najeriya, har yanzu ana samun matsin lamba a bangaren samar da wutar lantarki a kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

