'Yan Bindiga Sun Tafka Rashin Imani, Sama da Mutum 10 Sun Rasa Rayukansu
- 'Yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi yayin da suka kai farmaki wani ramin hakar ma'adanai a daren jiya Talata a jihar Filato
- Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa mutane 12 sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka bata bayan harin
- Kungiyar ilimi da al'adun Berom (BECO) ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce har yanzu ba a san adadin mutanen da suka bata ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum 12 daga cikin masu hakar ma'danan kasa yayin da wasu 'yan bindiga suka bude masu wuta a jihar Filato.
'Yan ta'addan, wadanda suka zo dauke da mugayen makamai sun aikata wannan danyen aiki ne a wani ramin hakar ma'adanai da ke garin Ratoso Fan, a karamar hukumar Barkin Ladi.

Source: Original
Mahara sun kashe masu hakar ma'adanai
Jaridar Leadership ta tabbatar da cewa akalla masu hakar ma'adai 12 aka tabbatar da sun rasa rayukansu a harin, wanda ya auku a daren ranar Talata da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar mazauna yankin, lamarin ya faru ne a daren Talata, lokacin da 'yan bindigar suka afka wurin hakar ma’adinan yayin da wadanda abin ya shafa ke tsaka da ayyukansu.
Majiyoyi sun bayyana cewa daga zuwan 'yan ta'addan, ba su yi wata-wata ba suka bude wa masu hakar ma'adanan wuta.
Sai dai Kungiyar Ilimi da Al’adu ta Berom (BECO) ta bayyana cewa har yanzu mutane da dama ba a san inda suke ba bayan harin da ‘yan bindigan suka kai.
Shugaban Kwamitin Ma’adinai na BECO a Karamar Hukumar Barkin Ladi, Dallang Davott, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
BECO ta tabbatar da batar mutane da dama
Ya ce ‘yan bindigan sun kai harin ne kan masu hakar ma’adinan a daren Talata yayin da suke tsakiyar aikinsu, cewar rahoton Ripples Nigeria.
Dallang ya ce:
“Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka bata ba, saboda lamarin ya faru ne da dare. ‘Yan bindigan sun afka wurin hakar ma’adinan tare da bude musu wuta.
“Saboda haka, da dama daga cikinsu sun tsere domin ceton rayukansu a lokacin harin. Amma zuwa yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane 12,” in ji shi.
A halin da ake ciki, yayin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato (PPRO), DSP Alfred Alabo, ta wayar tarho, bai dauka ba, haka kuma bai amsa sakonnin da aka tura masa ba.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kai hari coci a Kogi
A wani labarin, kun ji cewa ’yan bindiga sun kai hari cocin ECWA a yankin karamar hukumar Kabba/Bunu da ke jihar Kogi, aka sace wasu masu ibada da dama.
Mazauna yankin sun bayyana cewa da safiyar Lahadi ne ’yan bindigar suka shiga garin Àaaaz-Kiri, suna harbe-harbe, abin da ya tilasta wa mutane guduwa.

Kara karanta wannan
Za a sarara: Ranaku 3 da ƴan Najeriya za su samu hutu a Disamba 2025, Janairu 2026
Yayin wannan farmaki, an ce maharan sun kutsa kai har cikin cocin ECWA da ke gudanar da ibadar Lahadi, inda suka kai farmaki kan mutane.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
