Bayan Rasuwarsa, Aisha Ta Fadi Kuskuren Buhari cikin Mulkinsa Na Shekara 8

Bayan Rasuwarsa, Aisha Ta Fadi Kuskuren Buhari cikin Mulkinsa Na Shekara 8

  • Aisha Buhari ta yi tsokaci kan wasu abubuwan da suka faru a mulkin mijinta marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
  • A cikin bayanan da ta yi, ta bayyana yadda rayuwa ta kasance a fadar shugaban kasa lokacin da mijinta yake kan mulki a Aso Rock
  • Hakazalika ta bayyana kuskuren da marigayi Buhari ya yi a cikin shekaru takwas da ya kwashe yana mulkin Najeriya daga 2015 zuwa 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yi magana kan shekaru takwas na mulkin mijinta.

Aisha Buhari ta yi hukunci mai tsauri kan wa’adin shekaru takwas na mulkin mijinta, marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Aisha Buhari ta yi magana kan mulkin mijinta
Marigayi Muhammadu Buhari tare da Aisha Buhari Hoto: Aisha Buhari
Source: Facebook

Jaridar The Tribune ta ce kalamanta na kunshe ne a cikin wani littafi da aka kaddamar a fadar shugaban kasa, mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dr. Charles Omole ya wallafa.

Kara karanta wannan

Monguno ya tona yadda aka dakile shi a mulkin Buhari, ya kira sunayen mutum 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aisha ta yi magana kan mulkin Buhari

Tsohuwar uwargidan shugaban kasa ta ba da labarin yadda wasu ’yan tsirarun dattawa ’yan uwa da manyan masu fada a ji suka kewaye marigayi Buhari.

Aisha Buhari ta bayyana su a matsayin wani irin gungun mafia, masu amfani da dabaru domin cimma muradun kansu.

A cewar Aisha Buhari, halin da ta tsinci kanta a ciki ya kara tabarbarewa a shekarar 2017, wato shekaru biyu bayan fara wa’adin farko na marigayi shugaban kasa.

Ta ce a lokacin wasu manyan mutane sun gargadi Buhari cewa “karfin halayen matarsa” zai mamaye su idan aka ba ta dama, lamarin da ya kai ga shirin korar ta daga fadar shugaban kasa.

A cewar marubucin:

“Gidan ya cika da ’yan uwa da matansu da jikokinsu, tare da masu fada a ji da ma’aikata da suka koyi bin hanyoyin samun abin da suke so."
“Sun yi kokarin korar kowa, har da ni."

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Ta ce maganarta kai tsaye ce, kuma ta san tana da tsauri, amma ta tsaya kan iyakarta da cewa:

“Wannan gidana ne. Za ku iya zama a duk inda kuke so, amma ba za ku rika jagorantar ofishin mijina ba sannan kuma ku rika jagorantar da ni matarsa, a cikin gidana ba.”

Ta bayyana cewa tun da yawancin ’ya’yanta suna zaune kuma suna karatu a kasashen waje a farkon wa’adin mulkin Buhari, ’yan uwa na kusa sun cike gibin, inda suka mamaye gidaje a sassan fadar shugaban kasa.

Aisha ta ce Buhari ya yi kuskure a mulkinsa
Aisha Buhari tare da mijinta marigayi Muhammadu Buhari Hoto: @BuhariSallau1
Source: Twitter

Me Aisha ta ce kan kuskuren Buhari?

Kuma saboda kaunar da Buhari ke yi wa ’yan uwansa da tsofaffin abokansa, hakan ya sa ya zama wanda ake yi wa shisshigi da yaudara cikin sauki.

“Ana amfani da raunin da yake da shi wajen shirya masa makirci, wanda hakan ya jawo cikas ga manyan manufofin gwamnatinsa."
“Ya sa mutane marasa dacewa a muhimman wurare. Kuma bai canza su ba tsawon shekaru takwas.”

- Aisha Buhari

Buhari bai goyi bayan takarar Osinbajo ba

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare, Aisha Buhari ta bayyana cutar da ta yi ajalin Shugaba Buhari a Landan

A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana dalilin da ya sanya marigayi Muhammadu Buhari bai goyi bayan takarar Farfesa Yemi Osinbajo ba.

A cikin wani littafi da aka kaddamar, an bayyana cewa Buhari bai goyi bayan Osinbajo ba ne saboda ya yi mamakin yadda zai iya yin takara da Bola Ahmed Tinubu.

Marigayin bai mara wa mataimakinsa baya ba, sai ya bar wakilan jam'iyyar APC su zabi wanda suke so ya rike tutar jam'iyyar a zaben shugaban kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng