Maganganun Tinubu da Na Ministansa Sun Saba kan Kudin da Aka Samu a 2025
- Ministan kudi da tattalin arziki ya ce gwamnatin tarayya ta cimma N10.7trn kacal daga hasashen kudin shiga na N40.8trn a 2025
- Wannan ya sabawa ikirarin Shugaba Bola Tinubu da ya ce Najeriya ta cika burin kudin da ta ci burin samu a 2025 tun watan Agusta
- Wale Edun ya ce karancin kudin shiga ya tilasta wa gwamnati karbar rancen ₦14.1trn, lamarin da ya kara damun tattalin arziki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Kudi kuma Ministan Daidaita Tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana adadin kudin shiga da aka samu a shekarar 2025.
Edun ya ce gwamnatin tarayya ba ta cimma burin kudin shiga na shekarar 2025 ba, inda ya ce an samu Naira tiriliyan 10.7 kacal daga cikin Naira tiriliyan 40.8 da aka yi hasashe.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Source: Facebook
Maganganun Tinubu da ministansa sun sha bambam
Edun ya bayyana haka ne a jiya Talata 16 ga watan Disambar 2025 yayin wani zaman tattaunawa da Kwamitocin Majalisar Wakilai kan Kudi da Tsare-tsaren Kasa, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan furuci ya sabawa ikirarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda a baya ya bayyana cewa Najeriya ta riga ta cika burin kudin shiga na shekarar 2025 tun kafin karewar watan Agustan 2025.
Tinubu ya fadi hakan ne lokacin da yake jawabi ga mambobin Kungiyar Buhari Organisation da suka kai masa ziyara a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban ya ce shirin kara kudaden shiga daga bangaren da ba na man fetur ba ya yi tasiri matuka, har ya sa aka cimma hasashen kudin shiga na shekarar kafin lokaci.
Tinubu ya ce:
“A yau zan iya cewa da alfahari, Najeriya ba ta sake karbar bashi. Mun cimma hasashen kudin shigar shekarar nan tun watan Agusta."

Source: Twitter
Hasashen da aka yi na kudin shiga a 2025
An shirya zaman ne domin duba Tsarin Kashe Kudi na Tsakiyar Lokaci (MTEF) da Takardar Dabarun Kudi (FSP) na shekarun 2026–2028.
A cewar Edun, gwamnatin tarayya ta yi burin samun Naira tiriliyan 40.8 a matsayin kudin shiga na 2025 domin daukar nauyin kasafin Naira tiriliyan 54.9.
Sai dai ya ce kudaden da aka samu sun yi kasa sosai da hasashen da aka yi, inda ake sa ran kudin shigar shekarar zai tsaya ne a kusan Naira tiriliyan 10.7, cewar Premium Tmes.
“Alamomin da muke gani yanzu na nuna cewa kudin shiga na shekarar zai kare ne a kusan Naira tiriliyan 10.7, sabanin Naira tiriliyan 40.8 da aka tsara.”
- In ji Edun
Ministan ya danganta gibin kudaden shiga da raunin kudaden man fetur da iskar gas, musamman karancin harajin mai na PPT da kuma na kamfanonin mai da gas.
Tinubu ya magantu kan sabon haraji a Najeriya
Kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana ga ’yan Najeriya game da sababbin dokokin haraji da aka kawo.
Tinubu ya yi karin haske cewa dokokin haraji za su amfani talakawa, masu ƙaramin albashi da ’yan kasuwa a Najeriya.
Ya ce babu abin fargaba game da aiwatar da dokokin haraji, inda ya jaddada amfaninsu ga tattalin arziki da dimokuraɗiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

