Yadda Zanga Zangar 'Yan Kwadago ke Gudana a Kano, Sokoto, Sauran Jihohi
- Wasu mambobin kungiyar kwadago ta NLC sun taru a hedikwatarsu da ke Abuja domin zanga-zangar kasa baki daya kan matsalar tsaro
- Shugabannin kungiyar da na kungiyoyin farar hula sun bayyana a wuraren daban-daban, yayin da jami’an tsaro suka bazu domin sa ido
- A Kano, Sokoto Lagos da sauransu, ma’aikata sun fito kan tituna da sakonni masu nuna bukatar daukar matakan gaggawa kan matsalolin kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, ta aiwatar da zanga-zangar da ta shirya a fadin kasar nan domin nuna damuwa kan karuwar matsalolin tsaro da ke addabar ‘yan Najeriya.
A safiyar Laraba, mambobin kungiyar sun fara taruwa a hedikwatar NLC da ke Abuja, game da lura da yadda zanga-zangar za ta gudana.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe, sace-sace da garkuwa da mutane a sassa daban-daban na kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taro a hedikwatar NLC da ke Abuja
Daga cikin manyan wadanda suka hallara hedikwatar NLC a Abuja akwai shugaban 'yan kwadago, Joe Ajaero, tare da wasu shugabannin kungiyoyi.
Haka kuma, wasu jiga-jigan kungiyoyin farar hula sun bayyana, ciki har da Omoyele Sowore da ‘yan uwansa na kungiyar Revolution Now, wannan ya kara jawo hankalin jama’a.
Bayan isowarsu, shugaban NLC da wasu shugabannin kungiyoyin da ke karkashin NLC sun shiga wata ganawa, yayin da yawancin ma’aikata suka tsaya a harabar hedikwatar suna jiran umarni.
An yi zanga-zangan NLC a jihar Kano
Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, ta gudanar da zanga-zanga cikin lumana a birnin Kano a matsayin kira ga gwamnati domin magance matsalolin tsaro da ke shafar ma’aikata da ci gaban kasa.
Zanga-zangar ta kasance ba tare da rikici ko tashin hankali ba, inda mahalarta suka yi tattaki a titunan Kano kafin su isa harabar gidan gwamnati.
Matakin ya zo ne yayin da NLC ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ke shafar rayuwar ‘yan kasa, ayyukan yi da kuma bunkasar tattalin arziki.

Source: Facebook
Zanga-zanga ta barke a Lagos
Vanguard ta rahoto cewa a jihar Lagos, mambobin NLC sun fara zanga-zanga a safiyar Laraba a yankin Ikeja Underpass.
Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da rubuce-rubuce masu kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen matsalar tsaro cikin gaggawa.
Daga cikin sakonnin da aka gani akwai kira da ke cewa gwamnati ta daina bada uzuri da jawabi kawai, ta dauki mataki kai tsaye domin kare rayukan ‘yan kasa.
Masu zanga-zangar sun rera wakoki yayin da suke yawo a karkashin gadar Ikeja a lokacin da mutane suke wucewa.
Sokoto: An yi zanga-zanga da addu’o’i
A jihar Sokoto, NLC ta gudanar da nata zanga-zangar, inda mambobi suke dauke kwalaye masu kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen yakar ‘yan bindiga.
Kungiyar ta kuma hada da malamai domin gudanar da addu’o’i na musamman, tana bayyana hakan a matsayin mataki na karshe na neman taimakon Ubangiji domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Shugaban NLC a jihar, Abdullahi Aliyu Jungle, ya ce ta'addancin ‘yan bindiga ya yi matukar illata rayuwa da ci gaban al’umma a jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina da Kaduna.
Zanga-zangar kungiyar NLC a Anambra
A jihar Anambra ma, reshen NLC ya shiga zanga-zangar kasa baki daya a ranar Laraba, 17 ga Disamban 2025 kamar yadda the Nation ta rahoto.
Rahotanni sun nuna cewa zanga-zangar ta fara ne da misalin karfe 11:05 na safe daga sakatariyar NLC da ke Regina Caeli Junction, kafin ta kare a mashigar UNIZIK da ke Awka.

Source: Facebook
Shugaban NLC a Anambra, Humphrey Nwafor, ya ce sun fito ne domin jawo hankalin gwamnatin tarayya kan tabarbarewar tsaro a fadin kasar.
'Yan kwadago sun yi zanga-zanga a Rivers
A birnin Port Harcourt na jihar Rivers ma, mambobin NLC sun fito fili domin nuna goyon bayansu ga zanga-zangar kasa baki daya.
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da taron ne kusa da fadar gwamnati, inda aka jaddada bukatar daukar mataki kan matsalolin tsaro da ke shafar kasa baki daya.
Masu zanga-zangar sun fito a Kogi, Imo, Ebonyi da sauran jihohin Najeriya domin nuna damuwa game da halin da ake ciki a kasar.
Gargadin NLC kan taba masu zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yi gargadi da cewa za ta dauki mataki idan aka taba masu zanga-zanga a jihohi.
NLC ta ce za su fito zanga-zanga ne domin nuna damuwa game da yawan sace-sace da kai hare-hare a fadin kasar nan.
Kungiyar ta yi gargadi da cewa ko mutum daya aka taba a tawagar masu zanga-zanga za ta tsunduma yajin aiki nan take.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



