Matasa Sun Roki Barau Ya Yi Takara da Abba, Ana Son Ya Zama Gwamnan Kano
- Kungiyoyin matasa daga jihar Kano sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaban Kasa, Bola Tinubu domin wa’adi na biyu a 2027
- Sun kuma bukaci Sanata Barau Jibrin da ya tsaya takarar gwamna a babban zaɓen 2027 domin kawar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf
- Matasan a karkashin kungiyoyin sun bayyana muhimmancin manufofin da Bola Tinubu ya zo da su wajen kokarin inganta rayuwar 'yan Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata gamayyar ƙungiyoyin matasan Jihar Kano, karkashin inuwar Tinubu/Barau Support Group Coalition, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyoyin sun bayyana bukatarsu ga Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Haka kuma, ƙungiyoyin sun yi kira ga Sanata Barau Jibrin da ya tsaya takarar gwamnan Jihar Kano a zaɓen mai zuwa.

Source: Facebook
Wannan na ƙunshe ne a yayin wata ziyara da 'yan ƙungiyoyin suka kai Majalisar Tarayya da ke Abuja, inda suka gana da Sanata Barau Jibrin, kamar yadda ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2027: An goyi bayan Barau da Tinubu
A rubutun da Sanata Barau ya wallafa, ya tabbatar da cewa ziyarar ta gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Hafiz Liman, wanda shi ne shugaban gamayyar ƙungiyoyin.
A yayin ganawar, ƙungiyoyin sun jaddada cewa suna da cikakken tabbaci ga shugabancin Bola Ahmed Tinubu, tare da bayyana cewa yunƙurinsa na neman wa’adi na biyu ya dace da muradin ’yan Najeriya.
Sun ce aiwatar da 'Renewed Hope' ta Shugaba Tinubu ta fara haifar da sauye-sauye masu kyau, kuma za ta kawo ci gaba mai ɗorewa da wadata ga ƙasar nan idan aka ba shi damar kammala aikinsa.

Source: Facebook
Kungiyoyin sun yi kira kai tsaye ga Sanata Barau Jibrin da ya amsa kiran jama’a domin tsayawa takarar gwamnan Jihar Kano a 2027.
A cewarsu, Kano na bukatar shugabanci nagari da gogewa wanda zai haɗa kowa ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, addini ko yanki ba.
Matasa sun ba Barau lambar yabo
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta ƙunshi matasa ’yan gwagwarmaya daga dukkannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.
Sun ce 'ya'yansu sun fito daga addinai da kabilu daban-daban, ciki har da ’yan yankin Kudancin Najeriya da ke zaune a Kano, abin da ke nuna faɗin haɗin kai da karɓuwar ƙungiyar a tsakanin al’umma.
A cewar Hafiz Liman, shugaban ƙungiyar:
“Mu matasan Jihar Kano, ba tare da la’akari da bambance-bambance ba, mun amince da kai kuma mun goyi bayan ka domin tsayawa takarar gwamnan jiharmu. Bisa wannan dalili ne muke roƙon ka da ka fito takarar gwamnan Jihar Kano. Kuma, Insha Allah, za ka yi nasara.”
Ƙungiyoyin sun kuma bayyana rawar da suka taka wajen wayar da kan jama’a da tallata manufofi da ayyukan Shugaba Tinubu a fadin Jihar Kano.
Barau ya magantu game da tsaron Kano
A baya, mun wallafa cewa Sanata Barau I. Jibrin, mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya kuma Mataimakin Shugaban Majalisar, ya yi kakkausar suka kan harin da ‘yan bindiga suka kai jiharsa.
Barau Jibrin ya ce mazauna yankin sun shaida masa cewa ‘yan bindigan sun shigo ne daga wasu jihohin makwabta, kuma harin ya zo ne bayan makonni na kwanciyar hankali a yankin.
Sai dai Sanatan ya bayyana farin cikinsa da ceto mutum uku daga cikin biyar da aka sace, yana yabawa jami’an tsaro kan kwazonsu da jajircewarsu wajen kare rayukan talakawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


