NMDPRA: Farouk Ahmed Ya Yi Bayani game 'Martaninsa' ga Aliko Dangote

NMDPRA: Farouk Ahmed Ya Yi Bayani game 'Martaninsa' ga Aliko Dangote

  • Shugaban NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya musanta wata sanarwa da ake cewa ya fitar kan zarge-zargen da ake yi masa
  • Ya ce kalaman da ke yawo a kafafen sada zumunta ba daga gare shi suka fito ba, kuma ya kauce wa cacar baki a bainar jama’a
  • Farouk Ahmed ya bayyana kwarin gwiwar cewa binciken hukuma zai ba shi damar wanke sunansa gaba ɗaya daga zargin Aliko Dangote

FCT Abuja - Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya yi karin bayani game da sanarwar musanta zarge-zargen da Alhaji Aliko Dangote ke yi masa.

Sanarwar, wadda aka fitar a hukumance ta karyata wata sanarwa da ke yawo aka ce ya fitar da bayani dalla-dalla game da yadda ya samu kudin daukar nauyin karatun yaransa a kasashen waje.

Farouk Ahmed ya karyata martani ga Dangote
Alhaji Aliko Dangote tare da Farouk Ahmed Hoto: @zainab_Nasir00
Source: Twitter

Karin bayanin na kunshe a cikin wata sanarwa da hukumar NMDPRA ta wallafa a shafin X, a yayin da dambarwar Farouk Ahmed da Alhaji Aliko Dangote ke kara kamari.

Kara karanta wannan

NMDPRA: Dangote ya garzaya ICPC, ya nemi a kama babban jami'i a gwamnatin Tinubu

Farouk Ahmed ya karyata martani ga Dangote

A cikin sanarwar, Injiniya Farouk Ahmed ya ce an ja hankalinsa kan wata amsa da ake cewa ya bayar kan zarge-zargen da ake yi masa, amma ya jaddada cewa wannan sanarwa ba shi ya fitar da ita ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban NMDPRA ya kuma amince da cewa yana sane da zarge-zargen da ya bayyana a matsayin marasa tushe da ake yi masa da iyalansa, tare da hayaniyar da suka haddasa a cikin jama’a.

Duk da haka, ya ce a matsayinsa na shugaban hukuma mai kula da bangare mai matuƙar muhimmanci, ya yanke shawarar kauce wa shiga muhawara ko cacar baki a bainar jama’a.

Shugaban NMDPR na son a yi bincike

Injiniya Farouk Ahmed ya bayyana cewa wanda ke bayan zarge-zargen ya kai lamarin gaban wata hukuma ta bincike a hukumance.

Ya bayyana haka ne bayan lauyoyin Alhaji Aliko Dangote sun shigar da korafi a gaban hukumar ICPC suna neman a binciki Farouk Ahmed bisa zargin wadaka da dukiyar 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Borno da wani ya tashi bam, ya kashe sojojin Najeriya

Farouk Ahmed ya ce hukuma za ta wanke sunansa
Shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed Hoto: FB/NMDPRA
Source: Facebook

A cewarsa, wannan mataki zai ba da dama a tantance batutuwan cikin natsuwa da adalci, tare da bayyana gaskiya ba tare da son rai ba.

Ya ce yana da yakinin cewa binciken da ake gudanarwa zai taimaka wajen warware dukkannin shakku da kuma wanke sunansa daga duk wani zargi.

Farouk Ahmed, Shugaban hukumar NMDPRA, ya sake jaddada kudurinsa na ci gaba da gudanar da aikinsa cikin kwarewa da bin doka har sai gaskiya ta yi halinta.

Majalisa ta shiga batun Dangote da Farouk

A baya, mun wallafa cewa Majalisar Wakilan Najeriya ta ɗauki matakin shiga cikin rikicin da ya kunno kai tsakanin attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote da Injiniya Farouk Ahmed.

Majalisar ta yanke shawarar ba wa kwamitocinta damar gudanar da bincike game da rikicin da ke tasowa tsakanin manyan jami’ai a bangaren mai, inda ta bukaci a gano musabbabin rikicin cikin gaggawa.

'Dan majalisar tarayya mai wakiltar Askira Uba/Hawul a Jihar Borno, Hon. Midala Balami, ne ya gabatar da kudurin gaggawa a zaman majalisa, inda ya ce rikicin zai iya jawo matsala a farashin man fetur.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng