Barazanar Duhu na Tunkaro Najeriya kan Kalubale a Tashoshin Lantarki
- Kamfanoni sun fara rage samar da gas ga tashoshin wutar lantarki, lamarin da ke barazanar jefa ‘yan Najeriya cikin duhu a lokacin bukukuwan karshen shekara
- Masu rarraba wuta a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu sun sanar da abokan huldarsu cewa ana fuskantar raguwar wuta sakamakon matsalolin
- Duk da amincewar gwamnatin tarayya da biyan bashin masu gas a Najeriya, har yanzu ana samun matsin lamba a bangaren samar da wutar lantarki a kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Akwai alamun cewa ‘yan Najeriya na iya shafe lokacin bukukuwan karshen shekara cikin duhu, sakamakon karancin gas da ya fara shafar tashoshin samar da wutar lantarki a fadin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa wasu kamfanonin gas sun fara ragewa ko dakatar da samar da makamashin nasu ga tashoshin wuta, saboda basussukan da ake bin su, lamarin da ya janyo raguwar wutar lantarki a yankuna da dama.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa matsalar ta sake tayar da hankula, musamman ganin irin wahalhalun da jama’a suka sha a farkon shekarar 2024, lokacin da aka yi fama da rashin wuta sakamakon irin wannan matsala.
EEDC ya rage yawan wutar lantarki
A ranar Talata ne kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu, EEDC, ya sanar da kwastomominsa a yankin Kudu maso Gabas game da raguwar wutar lantarki.
A wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na kamfanin, Emeka Ezeh, ya fitar, an bayyana cewa karancin wutar ya samo asali ne daga matsalolin gas da ke shafar kamfanonin samar da wuta.
EEDC ta ce wannan halin ya tilasta wa kamfanin watsa lantarki na Najeriya rage raba wuta, wanda hakan ya rage yawan wutar da ake bai wa EEDC.
PHED ya rage yawan raba wutar lantarki
A baya ma kamfanin rarraba wutar lantarki na Port Harcourt ya fitar da sanarwa makamanciyar ta EEDC ga kwastomominsa.
Kamfanin ya bukaci abokan huldarsa da su yi hakuri, yana mai cewa ana aiki tukuru domin inganta samarwa da rabon wutar lantarki.
Bayanin kamfanonin samar da wuta
Shugabar kungiyar kamfanonin samar da wuta, Joy Ogaji, ta tabbatar da cewa matsalolin gas na shafar ayyukan tashoshin wutar lantarki.
Ta ce kamfanonin gas sun fara rage aiki ne saboda basussukan da ake bin su, duk da cewa sun dade suna ci gaba da samar da gas ba tare da biyan cikakken kudi ba.

Source: Twitter
A ranar 4, Disamba, 2025, gwamnatin tarayya ta sanar da amincewa da biyan Naira biliyan 185 domin biyan bashin gas, amma dalilin da ya sa aka cigaba samun matsalar bai fito fili ba har yanzu.
Lalata bututun gas zai shafi lantarki
A wani bangare, hukumar gudanar da tsarin wutar lantarki ta kasa, NISO, ta ce an samu karin raguwar wutar lantarki sakamakon lalata bututun gas.
The Cable ta rahoto cewa hukumar ta bayyana cewa lamarin ya katse isar gas zuwa wasu tashoshin wutar lantarki masu amfani da shi, wanda ya rage yawan wutar da ake samarwa a kasa.

Kara karanta wannan
Benin ta dawo hayyacinta, an daure sojoji da wasu mutum 30 bisa yunkurin juyin mulki
Wutar lantarki ta tayar da gobara a Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa wutar lantarki ta yi sanadin mummunar gobara a kasuwar Singa da ke jihar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ce ta tabbatar da labarin bayan wani bincike da ta gudanar a wajen da lamarin ya faru.
Jami'an gwamnatin Kano sun ziyarci kasuwar domin duba irin barnar da wutar ta jawo da kuma matakan da za a iya dauka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

