Yadda Mikel Obi Ya Kira Buhari da Kansa game da Alawus a Gasar Kofin Duniya

Yadda Mikel Obi Ya Kira Buhari da Kansa game da Alawus a Gasar Kofin Duniya

  • Tsohon kyaftin din Super Eagles, Mikel John Obi, ya ce ya kira fadar shugaban kasa domin alawus din ‘yan wasa
  • Mikel ya bayyana cewa NFF ta jinkirta biyan kudin ‘yan wasa tsawon watanni, lamarin da ya tilasta masa kai karar batun
  • Ya ce cikin sa’o’i 24 bayan kiran, an kawo kudin alawus din ‘yan wasan da jirgi na musamman aka raba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon kyaftin din kungiyar Super Eagles, Mikel John Obi, ya yi magana kan neman hakkin yan wasan Najeriya.

Obi ya ce ya tuntubi ofishin marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin tabbatar da cewa ‘yan wasan Najeriya sun karɓi alawus dinsu.

Mikel Obi ya tuna kiran Buhari da ya yi kan alawus in yan wasa
Tsohon dan wasan Najeriya, Mikel Obi da Muhammadu Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari, Pau Barrena/Getty Images.
Source: Facebook

Yadda NFF ta jinkirta biyan Super Eagles

Hakan na cikin wata hira da 'The Obi One Podcast' a Youtube inda ya nemowa yan wasan hakkinsu a gasar cin kofin duniya ta 2018 da aka yi a Rasha.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mikel ya ce Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta jinkirta biyan kudaden da ‘yan wasan suka samu daga cancantar shiga gasar.

Ya ce duk da alkawuran da jami’an NFF suka rika bayarwa kafin fara gasar, kudin ba su zo ba har sai da ‘yan wasan suka isa sansanin atisaye.

“Gabanin gasar kofin duniya, muna bin su bashin kudi. Mun dade muna tambaya tsawon watanni. Suna ce min, ‘Mikel, kada ka damu, za a biya idan kun zo sansani."

- Mikel Obi

Buhari ya ba yan wasan Super Eages alawus a gasar cin kofin duniya a 2018
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: UGC

Yadda Mikel Obi ya kira ofishin Buhari

Mikel ya kara da cewa bayan isa sansanin, ya sake tambayar sakataren kungiyar da shugaban NFF inda kudin yake, amma aka sake bashi amsar cewa komai zai daidaita.

Saboda haka, Mikel Obi ya ce ya kira marigayi Abba Kyari, wanda a wancan lokaci shi ne shugaban ma’aikatan fadar Buhari.

“Ina kiransa na ce masa akwai babbar matsala a kungiyar kasa. Dole ne a kawo kudin alawus din ‘yan wasa kamar yadda aka alkawarta."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama mutane 627, a jiha 1 kadai an kwato bindigogin AK 47 guda 27

- In ji Mikel

Ya ce cikin awa 24, wani jirgi na musamman ya sauka, aka kawo kudin zuwa otal din ‘yan wasan, aka mika shi hannu da hannu.

Matakin Mikel ya fusata hukumar NFF

Mikel ya ce an lissafta kudin kuma aka raba wa dukkan ‘yan wasan da suka taka rawa wajen cancantar shiga gasar washegari.

Ya kara da cewa matakin da ya dauka ya fusata wasu manyan jami’ai, ciki har da shugaban NFF a lokacin, wanda ya kira shi taro.

Ya ce:

“Suka ce min, ‘Mikel, me ya sa ka yi haka? Ka sa mun zama kamar jahilai.’ Na ce musu, ‘Ni tsawon watanni nake neman kudin nan."

Ya jaddada cewa kudin ba kyauta ba ne, illa hakkin da ‘yan wasan suka samu daga cancantar shiga gasar.

Aisha ta magantu kan rayuwa bayan mutuwar Buhari

An ji cewa Aisha Buhari ta ce rayuwa ta sauya tun bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mataimakin ciyaman a Zamfara bayan karbar kudin fansa

Ta bayyana cewa an rubuta littafin tarihin Muhammadu Buhari tun shekaru 10 da suka wuce kafin a sake ƙaddamar da shi.

Ta kuma karyata jita-jitar cewa Buhari wai Jibril ne daga Sudan, tana mai alakanta ta da raunin sadarwa da yada rade-radi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.