‘Dan wasa Mikel Obi ya yi rabon tallafin abinci ga Mabukata a Garin Jos

‘Dan wasa Mikel Obi ya yi rabon tallafin abinci ga Mabukata a Garin Jos

- ‘Dan wasa John Mikel Obi ya fito ya taimakawa marasa karfi a Najeriya

- Tsohon ‘Dan kwallon na Chelsea ya rabawa Mabukata kayan abinci a Jos

- Obi ya bada tallafin annobar COVID-19 ne ga mutanen Garin da ya tashi

Mun samu labari daga kafar sadarwar Instagram cewa ‘dan kwallon kafan Najeriya, John Obi Mikel ya bada tallafin kayan abinci ga Bayin Allah marasa karfi a garin Jos, da ke jihar Filato.

Shararren ‘dan wasan ya rabawa mutane buhunan shinkafa, wake, da taliya da sauran abinci. Tauraron ya yi wannan rabo ne a daidai lokacin da ake tsakiyar fama da annobar COVID-19.

Mikel Obi mai shekaru 33 a duniya ya tashi ne a garin Jos da ke tsakiyar arewacin Najeriya. Obi ya fara taka leda ne a matsayin babban ‘dan wasa a kungiyar Filato United kafin ya je Turai.

Yayin da cutar Coronavirus ta tsaida kasuwanci da sauran harkoki cak a fadin kasar nan, Mikel Obi ya kawo dauki ga mabukatan da ke Jos inda ya yi masu rabon abin da za su kai baka.

KU KARANTA: Jerin shararrun 'Yan kwallon kafan da COVID-19 ta sa su gaba

John Mikel Obi ya bayyana wannan aikin alheri da ya yi a shafinsa na sada zumunta na Instagram. Obi ya zaman Landan na tsawon shekaru goma inda ya bugawa Chelsea kwallo.

Tsohon ‘dan wasan tsakiyar na Chelsea ya rubuta: “Idan mu ka hada-kai, za mu iya bada taimako. Yau kenan a garin Jos. Inda na tashi.” Obi ya rubutawa wannan a shafinsa na Instagram.

A hoton da ‘dan kwallon ya wallafa, an gan shi cikin rigar tawagar Super Eagles ya na ba jama’a agaji. A daidai wannan lokaci dai musulman fadin Duniya su na azumin watan Ramadan.

Kawo yanzu dai Filato ba ta cikin wuraren da COVID-19 ta yi wa mugum kamu. Alkaluman hukumar NCDC sun tabbatar cewa mutane uku kadai aka samu dauke da cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel