Albishir da Shugaba Tinubu Ya Yi ga Talakawan Najeriya kan Sabon Haraji

Albishir da Shugaba Tinubu Ya Yi ga Talakawan Najeriya kan Sabon Haraji

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kwantarwa ’yan Najeriya hankulansu game da sababbin dokokin haraji da aka kawo
  • Tinubu ya yi karin haske cewa dokokin haraji za su amfani talakawa, masu ƙaramin albashi da ’yan kasuwa a Najeriya
  • Ya ce babu abin fargaba game da aiwatar da dokokin haraji, inda ya jaddada amfaninsu ga tattalin arziki da dimokuraɗiyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya abin farin ciki kan sabon dokar haraji.

Tinubu ya bayyana cewa sababbin dokokin haraji da gwamnatinsa ta samar za su amfani talakawa, masu ƙaramin albashi da kuma ’yan kasuwa.

Tinubu ya yi karin haske kan sababbin dokokin haraji a Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana aiki a ofishinsa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Haraji: Bola Tinubu ya ja hankalin jama'a

Tinubu, wanda Shugaban Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS), Dr. Zacheus Adedeji, ya wakilta, ya bayar da wannan tabbaci ne a jawabinsa a Taron Ajimobi Roundtable na 2025, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kwantar da hankalin jama’a kan fargabar aiwatar da dokokin harajin, inda ya ce babu wani abin tsoro game da su, inda ya bayyana cewa za a fara aiwatarwa daga shekara mai zuwa.

A cewarsa:

“Ina so in yi amfani da wannan dama in tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu abin fargaba game da sababbin dokokin haraji da za a fara aiwatarwa daga shekara mai zuwa.
“Dokokin na ɗauke da alheri ga talakawa, masu ƙaramin albashi da ƙananan ’yan kasuwa. Kamar yadda taken wannan taro ya nuna, dole ne al’umma su ci gaba da amincewa da dimokuraɗiyyarmu da ke ƙara bunƙasa.”
Tinubu ya kwantarwa al'umma hankali kan sababbin dokokin haraji
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a taro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya fadi halayen marigayi Sanata Ajimobi

Tinubu ya yaba wa masu gabatar da jawabi a taron, sannan ya jinjina wa Uwargidan Ajimobi, wadda aka naɗa jakadiya, cewar The Nation.

Game da marigayi Sanata Abiola Ajimobi, Tinubu ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen ɗan ci gaba wanda sadaukarwarsa ga dimokuraɗiyya ba ta taɓa kasancewa abin shakka ba.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye a Aso Rock

Ya ce Ajimobi ya yi wa jihar Oyo da Najeriya hidima ta musamman, inda ya kawo manyan ayyukan ci gaba, musamman ta fuskar sabunta birane da samar da tsaro.

Tinubu ya tunatar da jama’a cewa nasarar Ajimobi ta sake lashe zaɓe karo na biyu ta nuna irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo a Oyo.

Ya ƙara da cewa Ajimobi ya yi imani cewa shugabanci na buƙatar matakai masu tsauri a wasu lokuta, amma waɗanda ke haifar da ci gaba mai ɗorewa.

Saboda haka, Tinubu ya yi kira ga shugabanni da ’ya jam’iyyar APC a Oyo da su haɗa kai su ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan harajin 5%

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar harajin 5% a kan kayayyakin mai, wanda zai shafi fetur, dizal, da man jiragen sama.

Sabon tsarin zai shafi kowa daga 'yan acaba zuwa ‘yan kasuwa, malamai, dalibai da masu sana’o’i a fadin kasar nan.

Akwai bayani kan yadda harajin zai shafi rayuwar al'ummar Najeriya ta hanyoyi daban daban idan ya fara aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.