Danyen Mai Ya Yi Faduwar da bai Taba Yi ba cikin Shekaru 4 a Kasuwar Duniya

Danyen Mai Ya Yi Faduwar da bai Taba Yi ba cikin Shekaru 4 a Kasuwar Duniya

  • Farashin danyen mai a duniya ya fadi zuwa kasa da dala $60 kan kowace ganga karo na farko tun watan Fabrairun 2021
  • Rahotanni sun nuna fargabar yawan mai a kasuwa da yiyuwar sassauta takunkumin Rasha sakamakon tattaunawa da Ukraine
  • Duk da karuwar samar da mai a Najeriya, OPEC ta ce har yanzu kasar na kasa da adadin ganga 1.5m da aka ware mata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Rahotanni sun ce farashin danyen mai ya fadi a karon farko cikin shekaru hudu wanda ya girgiza kasuwannin duniya.

Farashin ya fadi zuwa dala $58 kan kowace ganga, karo na farko tun watan Fabrairun 2021.

Farashin danyen mai ya sake kasa a kasuwannin duniya
Ma'aikaci da ke aiki a matatar mai. Hoto: Bloomberg, Contributor.
Source: Getty Images

Yadda farashin danyen mai ya fadi a duniya

Rahoton TheCable ya ce lamarin da ya sake tayar da hankula a kasuwannin makamashi na duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun nuna cewa danyen man Brent, wanda shi ne ma’aunin farashin mai na duniya, ya fadi da kashi 2.86% zuwa dala $58.83 kan kowace ganga da misalin karfe 10:30 na dare.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Haka kuma, US West Intermidiate (WTI) ya ragu da kashi 2.88% zuwa dala $55.04 kan kowace ganga, cewar rahoton BusinessDay.

A cewar rahotanni, wannan faduwar farashi na da nasaba da damuwar yawaitar mai a kasuwa, tare da karuwar fatan cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, wanda hakan ka iya haifar da sassauta takunkumin da aka kakaba wa Rasha.

Rahoton ya kara da cewa masu sharhi a bankin Barclays na hasashen cewa farashin Brent zai kai matsakaicin dala $65 kan ganga a 2026, duk da kasancewar ana sa ran samun rarar mai kusan ganga miliyan 1.9 a kowace rana a kasuwa.

A ranar 30 ga Nuwamba, kungiyar OPEC ta tabbatar da barin adadin man da Najeriya ke hakowa a kan ganga miliyan 1.5 a rana har zuwa Disambar 2026.

Farashin gangar danyen mai ya fadi a kasuwanni
Ma'aikatan hakar danyen mai a bakin aiki. Hoto: Contributor.
Source: Getty Images

Matsayar wasu kasashe kan samar da mai

Haka kuma, OPEC ta ce kasashe takwas da suka hada da Saudi Arabia, Rasha, Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Kuwait, Kazakhstan, Algeria da Oman.

Kasashen sun sake jaddada matsayinsu na dakatar da karin samar da mai a watannin Janairu, Fabrairu da Maris na 2026, saboda dalilan yanayi da bukatar kasuwa.

Kara karanta wannan

Elon Musk ya zama mutumin farko a duniya da dukiyarsa ta haura $600bn

A ranar 12 ga Disamba, OPEC ta bayyana cewa samar da danyen mai a Najeriya ya karu a watan Nuwamba zuwa ganga miliyan 1.43 a rana, wanda shi ne mafi girma cikin watanni uku, amma har yanzu bai kai adadin da aka ware wa kasar ba.

A baya, Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da rage farashin ma’aunin danyen mai a kasafin kudin 2026 zuwa dala $60 kan ganga, daga tsohon hasashen dala $64.85.

Dangote ya sauke farashin litar mai

An ji cewa Matatar Dangote da manyan dillalan mai sun sauke farashin fetur zuwa N840 bayan danyen man Brent ya faɗi zuwa $62.

Rahoton masana’antu ya nuna cewa raguwar kuɗin tace mai ta sanya wa dillalan Najeriya sauya farashin sayar da fetur.

Wannan na zuwa yayin da kasashen OPEC+ suka tabbatar da dakatar da ƙarin samar da mai a Janairu zuwa Maris na 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.