'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake, sannan Sun Sace Tsohon Jami'in Kwastam
- ‘Yan bindiga sun kai hari a Ora da ke kan iyakar Osun da Kwara, inda suka kashe basarake tare da sace tsohon jami’in Kwastam
- Matar wanda aka sace ta ce harin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na yamma, kuma an sace tsohon jami'in a kofar gidansu
- Rundunar ‘yan sandan Osun ta tabbatar da harin, tare da bayyana matakan da ta dauka na ceto tsohon jami'in Kwastam da aka sace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Al’ummar Ora, wani gari da ke kan iyakar jihohin Osun da Kwara, sun tsinci kansu cikin firgici a ranar Litinin bayan wasu ‘yan bindiga sun kai masu mummunan hari.
Harin ya yi sanadin mutuwar wani basarake da aka bayyana sunansa da Dennis, yayin da aka sace wani tsohon jami’in Kwastam mai suna Emmanuel Owolabi.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kai hari Ora
Majiyoyi daga yankin sun shaida wa jaridar Punch cewa sace Owolabi ya jefa al’umma cikin tsoro, inda mutane suka rika gudu domin tsira da rayukansu, yayin da ‘yan bindigar suka tsere da wanda suka sace zuwa cikin daji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar wanda aka sace, Titilayo Owolabi, ta ce lamarin ya faru ne a gaban gidansu da ke Akisa Road, Ora, mintuna kaɗan kafin karfe 7:00 na yamma.
Ta bayyana cewa mijinta ya zo ya same ta a shagonta lokacin tana kokarin rufewa, sai ya tafi wani wuri a cikin garin, yayin da ita kuma ta koma gida domin girka abinci.
Titilayo Owolabi ta ce bayan ta gama girki tana shirin ba yara abinci, sai ta ji karar harbi a bakin gidansu, lamarin da ya tsoratar da su.
Yadda aka sace tsohon jami’in Kwastam
Ta bayyana cewa, da farko ta dauka mafarauta ne, amma daga baya harbin ya karu, sannan ta ji muryar mijinta a waje.
Ta ce:
“Na ji karar harbe-harbe, daga baya sai na ji muryar mijina a wajen katanga. Ban san cewa ‘yan bindiga sun rike shi ba. Na fita domin duba abin da ke faruwa.”
Ta kara da cewa daya daga cikin ‘yan bindigar ya tsallaka katanga zuwa cikin gidansu, yana magana da harshen Hausa.
“Na durkusa ina magana da shi da Hausa, amma sai ya fara duka na yana tambayata kudi. Suna ci gaba da harbe-harbe, daga baya sai na ji karar babur suna tafiya da mijina zuwa cikin daji."
- Titilayo Owolabi.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe basarake a harin
Wasu majiyoyi daga garin sun ce yayin da ‘yan bindigar ke tserewa, sun kashe wani basarake mai suna Dennis, wanda ke dawowa daga gonarsa.
An bayyana cewa an kashe shi ne a yankin Kwara, ba cikin Osun ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kai wannan farmaki.

Kara karanta wannan
Dakarun sojojin Najeriya sun bi sawun 'yan bindiga, sun gano mutane 3 a jihar Kano
Abiodun Ojelabi ya ce an tura karin jami’an tsaro tare da hadin gwiwar 'yan sa kai domin bincikar dazukan yankin don ceto tsohon jami'in Kwastam da kama masu laifin.
An bude wuta a wurin nadin sarauta
A wani labari, mun ruwaito cewa, rikicin nadin sabon sarki a kauyen Ido Ajegunle da ke ƙarƙashin karamar hukumar Esa-Oke a jihar Osun ya rikide zuwa tashin hankali.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya barke ne yayin da wasu 'yan bindiga suka bude wuta inda akalla jami’an ƴan sanda bakwai da wasu mazauna yankin suka jikkata.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami’an suna hanyar kai daukin gaggawa ne lokacin da aka kai musu farmaki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
