Jirgin Sama da Ya Taso daga Kaduna Ɗauke da Manyan Mutane Ya Yi Hatsari
- Wani karamin jirgin sama kirar Cessna 172 ya gamu da hatsari a filin jirgin Owerri bayan ya samu matsala a sararin samaniya
- Jirgin da ya taso daga Kaduna zuwa Port Harcourt ya yi kokarin sauka a Owerri saboda matsalar da ya samu, amma ya yi hatsari
- Hukumar NSIB ta ce gobara ba ta tashi ba bayan hatsarin, yayin da ta bayyana halin da mutane hudu da ke a jirgin suke ciki yanzu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Imo - Rahotanni da muka samu na nuni da cewa wani jirgin sama mallakin kamfanin Skypower Express ya yi hatsari a daren ranar Talata, 16 ga Disamba, 2025.
An ce jirgin ya yi hatsari ne a filin jirgin kasa da kasa na Sam Mbakwe da ke Owerri, jihar Imo, yayin da yake kokarin sauka bayan ya samu matsala a cikin sararin samaniya.

Source: UGC
Jirgin da ya taso daga Kaduna ya yi hatsari
Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare, inda jirgin kirar Cessna 172 mai rijista 5N-ASR ya yi hatsari a kan titin tashi da saukar jirage mai lamba, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya yi nuni da cewa mutane hudu ne ke cikin jirgin a lokacin da ya rikito kasa, ya yi katantawa tare yin rub da ciki.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi ne daga filin jirgin sama na Kaduna zuwa Port Harcourt, kafin matukan jirgin su sanar da cewa sun samu matsala a sararin samaniya.
Saboda wannan matsalar, suka karkatar da jirgin zuwa Owerri domin yin saukar gaggawa, amma sai ya rikito kafin saukar tasa ta kammala.
NSIB ta yi magana kan hatsarin jirgin
Zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, ba a tabbatar da ko an samu asarar rayuka sakamakon hatsarin jirgin ba.
Hukumar NSIB ta tabbatar da cewa jami’an ceto sun isa wurin hatsarin cikin gaggawa bayan faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
A cikin wata sanarwa da daraktar hulda da jama’a ta NSIB, Bimbo Oladeji, ta fitar, hukumar ta ce babu gobara bayan hatsarin jirgin, kuma hakan ya taimaka wajen hana asarar rai.
Hukumar ta kara da cewa ayyukan filin jirgin ba su tsaya ba, domin an ci gaba da amfani da filin sauka da tashin jirage.

Source: Twitter
An fara bincike kan dalilin hatsarin jirgin
Shugaban hukumar NSIB, Kyaftin Alex Badeh Jr., ya bayyana jin dadinsa da rashin asarar rai, yana mai cewa an fara aiwatar da ka’idojin bincike kamar yadda doka ta tanada.
Ya ce jami’an NSIB suna aiki tare da sauran hukumomi domin kare wurin hatsarin da kuma fara cikakken bincike kan tarkacen jirgin.
“Muna jajantawa kamfanin Skypower Express, kuma muna godiya ga Ubangiji da ba a samu asarar rai ba.
“Mun fara bincike, kuma za mu ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da muka samu.”
- Kyaftin Alex Badeh Jr.
Jirgin sojoji ya yi hatsari a Neja
A wani labari, mun ruwaito cewa, jirgin sama na rundunar sojojin Najeriya ya yi hatsari a Karabonde, cikin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa matukan jirgin sun samu nasarar fita lafiya tun kafin jirgin ya kife da yammacin Asabar, 6 ga Disamba, 2025.
Rundunar sojojin sama ba ta ce komai ba kawo yammacin sna yau amma an fara yada bidiyoyin yadda jirgin ya kama da wuta bayan hatsarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


