Ana Rade Radin DSS Ta Cafke Malamin Musulunci kan Zanga Zanga game da Falasdinu

Ana Rade Radin DSS Ta Cafke Malamin Musulunci kan Zanga Zanga game da Falasdinu

  • Wasu rahotanni sun yada cewa Hukumar DSS ta cafke malamin addinin Musulunci a jihar Osun bayan yada bidiyonsa kan Falasɗinu
  • An ce an kama Sheikh Daood Imran Molaasan, shugaban wata kungiyar Musulunci a Iwo, Osun, bayan wani bidiyon goyon bayan Falasɗinu
  • Sai dai shafin malamin ya fito ya yi karin bayani kan jita-jitar da ake yadawa domin kwantar wa al'umma hankali game da lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - An ruwaito cewa Hukumar Tsaro ta Farar Hula, DSS, ta kama Sheikh Daood Imran Molaasan a jihar Osun.

Sheikh Daood Molaasan shi ne shugaban wata kungiyar Musulunci da ke da hedkwata a Iwo, Jihar Osun wanda ke da dubban mabiya.

An karyata zargin kama malami kan goyon bayan Falasdinu
Sheikh Daood Imran yayin zanga-zanga game da Falasdinu. Hoto: The GRAND MUFTI of Yorubaland.
Source: Facebook

Sai dai shafin da ke yada bayanai game da malamin a Facebook ya karyata labarin cafke Sheikh Daood a daren yau Talata 16 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yada labarin cafke malamin Musuluncin

An ce an kama shi ya biyo bayan wani bidiyo a intanet inda shi da mabiyansa suka nemi ‘yantar da Falasdinu daga mamayar kasar Isra’ila, kamar yadda Ogun Update ya wallafa a Instagram.

Bidiyon Facebook da ya nuna suna daga tutar Falasdinu ya kara yaduwa sosai, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi da fargabar tsaro daga jama’a.

Kungiyar Ta’awunu Muslimeen ta bayyana kanta a matsayin mai koyar da addinin Musulunci da goyon bayan al’ummar Musulmi a duniya baki daya.

An ce kungiyar ta taba shirya makamantan zanga-zangan a baya, ciki har da wani taron goyon bayan Falasdinu da aka gudanar a shekarar 2018.

Abin da ya kara jan hankali a zanga-zangar

Wasu abubuwa a bidiyon, musamman amfanin da hannu wurin isan da sako sun jawo suka, inda wasu suka kwatanta shi da irin gaisuwar Nazi.

Bayyanar yara suna rera taken addini a yayin tafiyar ta kara tayar da hankali, ganin matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta kan tsattsauran ra’ayi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa Fulani makiyaya da harbi, an sace shanu 168 a Filato

Zuwa lokacin kammala wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwa ta hukuma kan dalilin kama jagoran kungiyar ba.

Malami ya musanta kamun DSS kan zanga-zanga game da Falasdinu
Taswirar jihar Osun da ke da mabambantan mabiya addinai. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da muka sani game jita-jitar kama malamin

Sanarwar da aka wallafa a shafin shehin malamin ya musanta labarin inda ya kwantarwa mabiyansa hankali da fargabar abin da suke ciki.

A cewar sanarwar:

"Sheikh Daood Imran Molaasan, Babban Mufti na Yorubaland, ba a kama shi ba, karya ne."

Bayan nan an fitar da bidiyo a shafin tare da tabbatar wa jama'a cewa DSS ba ta yi ram da malamin ba, akasin abin da yake yawo.

Masoyan malamin sun yi martani cikin farin ciki da samun labarin rahoton da ake yadawa a kafofin sadarwa karya ne.

Mafi yawansu suna bayyana jin dadi tare da jaddada jarumtakar shehin malamin da suke matukar mutuntawa a yankin.

Bauchi: 'Yan sanda sun kama malamin Musulunci

A baya, kun ji cewa 'yan sanda sun kama malami na makarantar Tsangaya bisa zargin azabtar da almajiri dan shekara 11 a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Kwamishinan yan sanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu ya ba da umarnin mika wanda ake zargi ga sashen binciken manyan laifuffuka.

A binciken farko da ya sanda aka yi, malamin ya ce ya daure yaron da igiya ne domin kada ya gudu kafin iyayensa su kariso.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.