NMDPRA: Dangote Ya Garzaya ICPC, Ya Nemi a Kama Babban Jami'i a Gwamnatin Tinubu
- Aliko Dangote ya bukaci ICPC ta binciki Farouk Ahmed bisa zargin rayuwa fiye da kudaden da yake samu a matsayin jami’in gwamnati
- Takardar ƙarar ta yi zargin cewa shugaban NMDPRA din ya kashe sama da dala miliyan bakwai kan karatun ’ya’yansa hudu a Switzerland
- Dangote ya ce zargin ya shafi cin hanci, karkatar da kudaden gwamnati da karya dokar ka’idojin halayen jami’an gwamnatin Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya shigar da ƙara a gaban hukumar ICPC kan zarge-zargen da yake yi wa shugaban hukumar NMDPRA, Engr. Farouk Ahmed.
A cikin takardar ƙarar da aka rubuta kuma aka miƙawa ICPC a ranar 16 ga Disamba, 2025, Dangote ya ce yana zargin Farouk kan cin hanci da kashe kudaden da suka zarce albashinsa.

Source: UGC
Dangote ya nemi a kama shugaban NMDPRA
Takardar da aka mikawa ICPC ta hannun lauyansa, Ogwu Onoja, SAN, attajirin dan kasuwan ya ce wadannan zarge-zarge sun cancanci a kama Farouk, a bincike shi tare da gurfanar da shi a kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar ƙarar, wadda ofishin shugaban ICPC, Musa Aliyu, SAN, ya karɓa, ta yi zargin cewa Farouk ya kashe sama da dala miliyan bakwai wajen biyan kudin karatun ’ya’yansa hudu a makarantu daban-daban na ƙasar Switzerland.
Dangote ya ce an biya kudaden ne gaba ɗaya na tsawon shekaru shida, ba tare da wata hujjar halastacciyar hanyar samun kudin da za ta iya bayyana irin wannan kashe-kashen ba daga jami’in gwamnati.
Zargin cin hanci da karkatar da kudin jama’a
A cewar takardar, Farouk ya saba wa tanade-tanaden Dokar Ka’idojin Halayen Jami’an Gwamnati, inda ake zarginsa da cin hanci da almubazzaranci da kudaden jama’a har ya kai miliyoyin daloli.
Dangote ya kuma yi zargin cewa shugaban NMDPRA ya yi amfani da mukaminsa wajen karkatar da kudaden gwamnati domin amfanin kansa da na iyalansa.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi
Attajirin ya jaddada cewa Farouk ya shafe duk rayuwarsa wajen aiki a bangaren gwamnati, kuma ba zai yiwu kudaden shigarsa na halal su kai adadin da ake zargin ya kashe ba, in ji rahoton The Cable.

Source: Twitter
Dangote ya nemi ICPC ta binciki Farouk
Dangote ya ce ICPC na da ikon bincike da gurfanarwa a karkashin sashe na 19 na dokarta, inda hukuncin laifin ya kai daurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin tara ba.
Dangote ya bayyana kwarin gwiwarsa ga hukumar ICPC da sauran hukumomin yaki da cin hanci, yana mai cewa zai bayar da cikakkun hujjoji don tabbatar da zarge-zargen cin hanci, cin zarafi da almubazzaranci da ake yi wa shugaban NMDPRA.
Ya bukaci hukumar da ta dauki mataki cikin gaggawa, ganin cewa lamarin ya riga ya shiga idon jama’a, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki kan duk wanda aka samu da laifi.
Majalisa ta nemi a dakatar da Farouk
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan majalisar wakilai sun baukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da shugaban NMDPRA kan rikicinsa da Aliko Dangote.
'Yan majalisar wakilan sun ce babu gaskiya a duk zarge-zargen da Farouk yayi game da matatar Dangote domin a gabansu an yi gwajin dizal ɗin matatar.
Sun zargi Farouk Ahmed da rashin iya aiki tare da zagon ƙasa ga matatar cikin gida yayin da suke bada lasisin shigo da dizal mara kyau daga kasashen waje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

