An Gano Dalilin da Ya Sa Buhari Ya Sauya Fasalin Naira daf da Zaɓen Tinubu a 2023

An Gano Dalilin da Ya Sa Buhari Ya Sauya Fasalin Naira daf da Zaɓen Tinubu a 2023

  • Wani sabon littafi da aka wallafa ya bayyana dalilin da ya sa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin Naira
  • Wani bangare na littafin ya ce an yi sauyin fasalin ne domin dakile sayen kuri’u, ba don cutar jam’iyya mai mulkin Najeriya ba
  • Littafin ya ce hukumomin tsaro sun nuna damuwa kan rawar da kudi ke takawa a zabe, inda EFCC ta gabatar da shawarar takaita amfani da tsabar kudi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da manufar sake fasalin Naira ne domin yaki da sayen kuri’u.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi sauyin fasalin ne saboda zabe, ba don kawo cikas ga wata jam’iyyar siyasa ba.

An fadi dalilin Buhari na sauya fasalin Naira
Marigayi Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Muhammadu Buhari, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Wannan bayani na kunshe ne a cikin sabon littafi mai taken 'From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari', wanda Dr. Charles Omole ya rubuta, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare, Aisha Buhari ta bayyana cutar da ta yi ajalin Shugaba Buhari a Landan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da ake yi wa Buhari kafin zaben 2023

Wannan na zuwa ne bayan zarge-zargen cewa an kawo maganar sauya fasalin Naira ne domin jawo wa Bola Tinubu tangarda a zaben 2023.

Ko da fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin, ana ganin hakan bai rasa nasaba da yar matsala da ta so afkuwa tsakanin Buhari da Bola Tinubu daf da zaɓen.

Duk da ƙoƙarin sauya fasalin Naira domin rage sayan kuri'u a zaben, hakan bai hana komai ba domin an yi barna da kudi kuma an sayi mutane da dama da kudi har ma da kayan abinci.

Buhari ya yi kokarin hana sayan kuri'u a zaben 2023
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: Facebook

'Dalilin sauya fasalin Naira a mulkin Buhari'

Littafin ya bayyana cewa manufar sake fasalin Naira ta jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ‘yan siyasa suka fassara ta a matsayin yunkurin cutar da APC kafin zaben 2023.

Sai dai littafin ya ambato tsohon daraktan DSS, Yusuf Bichi, wanda ya ce hukumomin tsaro sun damu da yadda ake amfani da tsabar kudi wajen magudin zabe.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye a Aso Rock

A cewar littafin, tsohon shugaban EFCC ne ya gabatar da shawarar sake fasalin Naira domin rage amfani da kudi wajen sayen kuri’u a lokacin zabe.

Buhari ya amince da hujjar da aka gabatar masa, yana mai jaddada cewa doka ba za ta fifita ko tauye wani dan siyasa ko jam’iyya ba, cewar Punch.

Littafin ya kara da cewa Buhari ya ba da umarnin sake duba aiwatar da manufar, yana mai jaddada cewa yakar tasirin kudi a zabe ne babban buri.

Tinubu ya sa Buhari bai 'yi' Osinbajo ba

Mun ba ku labarin cewa yan Najeriya da dama sun yi tsammanin tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai gaji kujerar Muhammadu Buhari.

Shi kansa Yemi Osinbajo ya so ya dare kujerar mai gidansa a zaben 2023 kafin zuwan Bola Tinubu wanda ya yi nasara har a babban zabe.

Sai dai a cikin wani sabon littafi da aka rubuta, an bayyana cewa Buhari bai goyi bayan takarar mataimakin nasa ba saboda fitowar Bola Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.