Sabon Tarihi: Najeriya Za Ta Karbi Jiragen Yaki Mafi Girma a Afirka Ta Yamma daga Italy

Sabon Tarihi: Najeriya Za Ta Karbi Jiragen Yaki Mafi Girma a Afirka Ta Yamma daga Italy

  • Najeriya na shirin karɓar jiragen yaƙi M-346 guda 24 daga ƙasar Italiya, bayan yarjejeniya da kamfanin tsaro na Leonardo
  • An ce yarjejeniyar, wadda ta kai fiye da triliyan biyu, ita ce mafi girman sayan jiragen soji a yankin Afirka ta Yamma
  • Rundunar Sojin Sama ta ce jiragen za su ƙarfafa horaswa da ayyukan yaƙi, musamman a yaƙin Boko Haram da ’yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Najeriya ta kulla yarjejeniya da wani kamfani a kasar Italy a kokarin ci gaba da yaki da ta'addanci a kasar.

Kasar na shirin karɓar jiragen yaƙi samfurin M-346 guda 24 daga ƙasar Italiya domin ƙarfafa rundunar sojin sama.

Najeriya za ta karbo jiragen yaki da ta biya kudinsu
Samfurin jirgin yaki da Najeriya ta saya daga Itali, Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, fmino.gov.ng.
Source: Facebook

Najeriya ta kulla yarjejeniya kan tsaro, ta'addanci

A watan Nuwambar 2023 ne Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kulla yarjejeniya da kamfanin tsaro na Italiya, Leonardo, domin samar da waɗannan jiragen yaƙi, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

An jero 'zunuban' da marigayi Buhari ya aikata a mulkinsa daga 2015 zuwa 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar ta kai kimanin Naira tiriliyan biyu, kuma ana kallonta a matsayin mafi girman sayan jiragen soji da aka taɓa yi a yankin Afirka ta Yamma.

Yarjejeniyar ta haɗa da shekaru 25 na tallafin kayan aiki da gyara, inda kamfanin Leonardo zai kasance shi kaɗai ke da hurumin kula da ayyukan gyaran jiragen.

Tsare-tsaren da ke cikin jiragen yakin

Jiragen M-346 na da wuraren ɗora makamai guda bakwai, kuma suna iya ɗaukar makaman ta sama-da-sama da sama-da-ƙasa, tare da na’urorin hangen nesa da ake haɗawa da hular matukin jirgi.

A halin yanzu, jirage guda shida ana ci gaba da kera su a Italiya, inda ake sa ran za a kawo uku daga cikinsu zuwa Najeriya a shekarar 2025, yayin da sauran za su iso kafin tsakiyar 2026.

Najeriya na ci gaba da shirin domin yaki da ta'addanci
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Dàda Olusegun.
Source: Facebook

Amfanin da jiragen za su yi wa sojoji

Shugaban Rundunar Sojin Sama a lokacin kulla yarjejeniyar, Air Marshall Hasan Abubakar, ya bayyana cewa jiragen za su ƙara ƙarfafa horaswar matuka jirgi da kuma inganta ayyukan soji a fannoni daban-daban.

Kara karanta wannan

An fara gunaguni bayan mai tsaron Tinubu ya zama Birgediya Janar a soja

Ya ce sayen jiragen na daga cikin ƙoƙarin da Najeriya ke yi na ƙarfafa tsaro, musamman a yankin Arewa maso Gabas inda ake yaƙi da Boko Haram da ISWAP.

Haka kuma, jiragen za su taimaka wajen yaƙi da satar mutane da ayyukan ’yan bindiga da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar nan.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta jaddada cewa wannan mataki na daga cikin manyan dabarun gwamnati na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Najeriya ta duba jiragen yaki a ketare

A baya, an ji cewa tsohon ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya ziyarci masana’antun Italiya, inda ake kera jiragen yakin sojojin saman Najeriya.

Akwai jiragen AW109 Trekker guda 10 da jiragen M-346 Fighter Jets guda 24 da ake haɗawa don ƙarfafa rundunar sojin

Wannan mataki na cikin shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na inganta tsaron ƙasa da sabunta kayan aikin soja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.