Jita Jita Ta Kare, Aisha Buhari Ta Bayyana Cutar da Ta Yi Ajalin Shugaba Buhari a Landan

Jita Jita Ta Kare, Aisha Buhari Ta Bayyana Cutar da Ta Yi Ajalin Shugaba Buhari a Landan

  • Hajiya Aisha Buhari ta yi bayanin cutar da ta zama ajalin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a littafin da aka kaddamar
  • Asiha ta musanta rade-radin da mutane suka rika yadawa cewa guba ta yi ajalin Buhari, ta ce wannann labari ba gaskiya ba ne
  • A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025 ne Allah ya karbi ran Buhari a asibitin da yake jinya a birnin Landan na kasar Birtaniya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohuwar uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta kawo karshen jita-jitar da aka rika yadawa kan abin da ya yi ajalin marigayi Muhammadu Buhari.

Bayan rasuwar Buhari, mutane sun rika yada jita-jitar cewa gubar da aka sa masa tun yana matsayin shugaban kasa ce ta zama ajalinsa.

Buhari da mai dakinsa, Aisha.
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da matarsa, Aisha Buhari Hoto: Aisha Buhari
Source: Facebook

Sai dai a rahoton da Leadership ta kawo, Aisha Buhari, ta karyata jita-jita da raɗe-raɗin da ke cewa marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya mutu ne sakamakon gubar da aka sa masa.

Kara karanta wannan

'Buhari ya zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace cuta ta yi ajalin Buhari a Landan?

Matar marigayin ta bayyana cewa likitoci sun sanar da su iyalansa cewa cutar huhu (pneumonia) ce ta yi sanadin rasuwar Shugaba Buhari.

Hakan dai na cikin bayaninta da ke cikin sabon littafin da aka kaddamar na tarihin Buhari mai suna, “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari."

Aisha Buhari ta ce babu ƙamshin gaskiya a cikin zargin guba, shakar wani abu a na’urar sanyaya yanayi (AC), ko wata makarkashiya ta ɓoye dangane da mutuwar mijinta.

Ta bayyana irin waɗannan labarai a matsayin tsoratarwa da ke karkatar da hankali daga ainihin matsalolin kula da lafiya.

A cewarta, likitocin da suka kula da tsohon shugaban ƙasar sun bayyana wa iyalansa karara cewa cutar pneumonia, wacce ke taba huhu ce ta yi sanadin mutuwarsa.

Abubuwan da mutane suka yada

Ta ce a lokacin, rahotannin jama’a sun bambanta, wasu kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa ya yi doguwar jinya, wasu kuma sun ce gajeriyar jinya ce, yayin da wasu kaɗan suka ambaci cutar sankarewar jini.

Kara karanta wannan

Tonon silili: Aisha Buhari ta fadi kuskuren da mijinta ya yi a lokacin mulkinsa

Sai dai ta ce iyalan marigayi Muhammadu Buhari sun dogara ne da bayanin da likitoci suka ba su kai tsaye.

Littafin ya gabatar da bayanin da Aisha Buhari ta yi tare da waɗannan rahotannin kafafen yaɗa labarai.

Muhammadu Buhari da Aisha.
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da matarsa, Aisha Hoto: @MBuhari, Aisha Buhari
Source: Twitter

Halin da Aisha Buhari ke ciki yanzu

Game da rayuwa bayan barin mulki, Aisha Buhari ta ce ta zaɓi rayuwa mai sauƙi da natsuwa, inda ta fi mayar da hankali kan iyali da yi wa al'umma hidima, amma ba siyasa ba.

Ta bayyana cewa gidauniyarta ta kafa cibiyar kula da cututtukan zuciya da lafiya a Kano, wadda ta gudanar da fiye da ayyukan jinya 200, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Aisha ta tuna jinyar Buhari a 2017

A wani rahoton, kun ji cewa Aisha Buhari ta ce ba guba ba ce ta jawo rashin lafiyar da ta kai shugaba Muhammadu Buhari jinyar kwanaki 154 a 2017 a Landan.

Ta jaddada cewa mijinta bai kamu da wata cuta ba, illa dai tangarda da aka samu a tsarin abinci da shan magani da ta saba kula da su tun kafin su koma fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana dalilin Buhari na kin goyon bayan takarar Osinbajo a 2023

A cewar Aisha Buhari, yada jita-jitar cewa tana shirin kashe mijinta ta yi tasiri har ta kai ga jefa Buhari cikin shakku na wani lokaci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262