Tonon Silili: Aisha Buhari Ta Fadi Kuskuren da Mijinta Ya Yi a Lokacin Mulkinsa

Tonon Silili: Aisha Buhari Ta Fadi Kuskuren da Mijinta Ya Yi a Lokacin Mulkinsa

  • Aisha Buhari ta bayyana dalilan da suka sa marigayi tsohon shugaban kasa bai sallami ministoci da hadimansa da suka gaza a aiki ba
  • Uwargidan tsohon shugaban kasar ta ce tsufa da tsoron a kira shi 'mai kama-karya' sun sa Muhammadu Buhari ya yi taka-tsantsan a mulkinsa
  • Sai dai, bayan sauka daga mulki, EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin Buhari kan zarge-zargen almundahanar biliyoyin Naira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Uwargidan tsohon shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana dalilan da suka sa marigayi Muhammadu Buhari, bai cika sallamar ministocu da hadimansa da ba sa aiki yadda ya kamata ba.

Ta kuma bayyana yadda Buhari ya kan roki sabuwar gwamnati a madadin wasu daga cikin abokansa da ‘yan uwansa da ke fuskantar bincike, domin kare su daga matsin lamba.

Kara karanta wannan

Bayan gama idda, Aisha Buhari ta yi matsaya kan sake aure

Aisha Buhari ta fadi dalilan da suka sanya Buhari bai sallami ministocin da suka gaza aiki ba.
Aisha Buhari tare da tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: @Buharisallau1
Source: Twitter

Wannan bayani na Aisha Buhari na cikin wani sabon littafin tarihin Buhari mai shafuka 600, wanda Dr Charles Omole ya rubuta da aka kaddamar a Abuja, in ji rahoton Punch.

Me ya sa Buhari bai sallami ministoci ba?

Littafin, mai babi 22, ya yi duba kan rayuwar Buhari tun daga yarintarsa a Daura, jihar Katsina, har zuwa rasuwarsa a wani asibiti a Landan a tsakiyar watan Yulin 2025.

A cewar uwargidan Buhari, tambayar da ta fi damun gwamnatinsa ita ce: “Me ya sa ba a sauya ministoci ko shugabannin tsaro da suka gaza tabuka abin kirki ba?”

Ta bayar da hujjoji guda biyu: tsufan Buhari da kuma tsoron kakaba masa sunan “mai mulkin kama-karya” da aka rika danganta shi da shi tun shekarun 1980.

Ta ce Buhari yakan ce, idan mutum ya tsufa to karfin aikinsa kan ragu, haka kuma yakan ji tsoron cewa idan ya sallami wani, mutane za su fara zarginsa da nuna tsauri a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Yadda hadiman Buhari suka so ayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC a zaben 2023

Abin da ake gani kuskure a mulkin Buhari

Aisha Buhari ta ce wasu da ke kusa da Buhari sun koyi amfani da wannan halin nasa, suna yi masa maganganu da ke kara masa shakku wajen daukar matakan sauye-sauye.

Ta ce:

“Ko da mutum yana cin hanci, idan har yana iya yin kashi 50 cikin 100 na aiki, to za a kyale shi. Amma idan yana cin hanci kuma ba ya aiki, to dole ne a sallame shi.”

Marubucin littafin, Dr. Omole, ya ce wannan bayani na Aisha ya kara haske kan dalilin da ya sa Buhari ya kasance mai jinkiri wajen korar jami’an gwamnati, yana mai cewa Aisha ta amince cewa wannan kuskure ne a gwamnatinsa.

Aisha ta ce Muhammadu Buhari ya kasance yana kare wasu makusantansa da jami'an gwamnati da ya kamata su fuskanci tuhuma kan abubuwan da suka aikata.

"Daga baya, na gano cewa lokacin da aka bukaci ya bar hukumomi su yi bincike kan zarge-zargen rashawa, Buhari ya rika rokon gwamnati mai ci a madadin makusantansa.

Kara karanta wannan

Matar Buhari, Aisha ta fadi yadda iyalansa ke rayuwa bayan rasuwarsa

"Ya rika kokari don kare su daga dukkan tuhume-tuhume saboda har a lokacin yana dogara da su ne a wasu harkokinsa na rayuwa."

- Aisha Buhari.

Aisha Buhari ta ce Buhari ya kasance yana kare wasu daga cikin hadimansa don kar a bincike su.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a lokacin yana kan mulki. Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Binciken jami’an gwamnatin Buhari bayan 2023

Tun bayan barin mulki a 2023, hukumar EFCC ta kasance tana binciken wasu jami’an gwamnatin Buhari. Daga cikinsu akwai tsohon Akanta-Janar Ahmed Idris, wanda ake tuhuma da almundahanar N109bn.

Haka kuma, tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, ya fuskanci zargin karkatar da kusan N22bn da suka shafi ayyukan Zungeru da Mambilla.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, shi ma yana gaban kotu kan zarge-zargen kwangiloli da suka kai biliyoyin Naira.

Bugu da kari, tsohuwar Ministar Harkokin Jin Kai, Sadiya Umar-Farouq, ta fuskanci tambayoyi kan kashe N37.1bn, yayin da tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami, ya shiga bincike kan batun kudin Paris Club da suka kai kusan $418m, duk da cewa ya musanta zargin.

Abin da ya jawo rashin lafiyar Buhari

A wani labari, mun ruwaito cewa, Aisha Buhari ta yi magana kan rashin lafiyar da ta tilasta marigayi Muhammadu Buhari daukar hutun jinya na tsawon kwanaki 154 a 2017.

Kara karanta wannan

Aisha ta fadi yadda 'cin abinci' ya jawo wa Buhari rashin lafiya a 2017

Aisha ta jaddada cewa mijinta bai kamu da wata cuta ba, illa dai katsewa da tangarda a tsarin abinci da shan magani da ta saba kula da su tun kafin su koma zama a fadar Aso Rock.

Uwargidan tsohon shugaban kasar ta ce jikin tsofaffi na bukatar kulawa, tana mai cewa Buhari ba shi da wata cuta mai tsanani, kawai yana bukatar kiyaye masa tsarin shan magani ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com