Magana Ta Fito: An Bayyana Dalilin Buhari Na Kin Goyon Takarar Osinbajo a 2023

Magana Ta Fito: An Bayyana Dalilin Buhari Na Kin Goyon Takarar Osinbajo a 2023

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya so ya gaji kujerar marigayi Muhammadu Buhari
  • Sai dai a cikin wani sabon littafi da aka rubuta, an bayyana cewa Buhari bai goyi bayan takarar mataimakin nasa ba
  • A cikin littafin an bayyana dalilin da ya sa Buhari ya ki yarda ya goyi bayan takarar Osinbajo ta shugaban kasa

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Marigayi Muhammadu Buhari bai goyi bayan burin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ba.

A cewar wani sabon littafi, Buhari bai goyi bayan Osinbajo ba ne sakamakon kasancewar Bola Tinubu a cikin masu takarar neman kujerar.

Buhari bai goyo takarar Osinbajo ba a zaben 2023
Farfesa Yemi Osinbajo tare da marigayi Muhammadu Buhari Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce an bayyana wannan bayani ne a cikin littafin “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dr Charles Omole ya rubuta.

Kara karanta wannan

Bayan gama idda, Aisha Buhari ta yi matsaya kan sake aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kaddamar da littafin ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025 inda ya yi bayani dalla-dalla kan rayuwar Buhari, tarihinsa a aikin soja, da kuma tafiyarsa a harkar siyasa.

Meyasa Buhari bai goyi bayan Osinbajo ba?

A cewar Omole, Buhari ya ga lamarin a matsayin abin mamaki yadda Osinbajo zai iya tsayawa takara tare da Bola Tinubu ta wannan hanya.

Omole ya ambato Buhari yana cewa:

"Ban san Osinbajo daga ko’ina ba, na hadu da shi ne kawai ta hannun Tinubu.”

Ya rubuta cewa an dauki zabin Tinubu a matsayin sakayya bisa rawar da ya taka a matsayin uban gida da kuma mai daukar nauyin jam’iyyar APC.

A cewar Omole, akwai hadin baki na adawa da Tinubu a tsakanin wasu manyan masu fada a ji a gwamnatin Buhari.

“Majiyoyi sun kuma ce Buhari bai ji dadin yadda Osinbajo bai ‘tuntube shi’ ko ya nemi shawararsa ba kafin ya shiga takara. Maimakon haka, Osinbajo ya dai ‘sanar’ da shi ne kawai.”

Kara karanta wannan

Yadda hadiman Buhari suka so ayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC a zaben 2023

“An ambato Shugaban kasa yana tambayar yadda mataimakinsa zai iya tsayawa takara a fili yana kalubalantar wanda ya taimaka masa."

- Charles Omole

Buhari bai goyi bayan kowane dan takara ba a zaben fitar da gwani na APC
Tsohon shugaban kasar Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

Aisha Buhari ta goyi bayan Tinubu

Omole ya kara da cewa goyon bayan da A’isha Buhari ta ba Tinubu gabanin zaben 2023 ya jawo fushin wasu manyan masu fada a ji a karkashin mulkin Buhari, amma uwargidan shugaban kasar ba ta damu da hakan ba.
“Goyon bayan da A’isha Buhari ta nuna wa takarar Tinubu ya kalubalanci karfin masu fada a ji. Duk da haka, ba ta damu ba."
"Ganin irin dagewar ta, Tinubu ya kai mata ziyara tare da rokon ta taimaka masa wajen shirya yakin neman zaben mata tare da matarsa, Sanata Remi Tinubu. Ta amince, kuma aka kafa kwamitin yakin neman zaben mata na APC.”

- Charles Omole

An yi karya da sunan Buhari a 2023

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu hadiman marigayi Muhammadu Buhari sun yi masa karya kan zaben shekarar 2023.

An bayyana cewa hadiman sun ba da umarnin bogi da ke nuna cewa Buhari ya amince Ahmad Lawan ya zama dan takarar shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

Barau ya bukaci a dauki matakin gaggawa game da harin 'yan bindiga a Kano

Sai dai, Buhari da kansa ya musanta hakan inda ya nuna cewa wannan magana ba daga bakinsa ta fito ba domin bai goyon bayan kowane dan takara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng