Bayan Gama Idda, Aisha Buhari Ta Yi Matsaya kan Sake Aure

Bayan Gama Idda, Aisha Buhari Ta Yi Matsaya kan Sake Aure

  • Aisha Buhari ta bayyana dalilanta na yanke shawarar kin sake aure bayan rasuwar tsohon mijinta, tana cewa shawarar ta fito ne bayan tunani mai zurfi
  • Sabon littafin tarihin rayuwar Muhammadu Buhari ya haska yadda uwargidan ta ke kallon makomar rayuwarta bayan rasuwar mijinta a tsakiyar 2025
  • Ta kuma bayyana tsare-tsarenta na gaba da suka shafi kula da iyali, ayyukan jin kai da kuma rayuwa cikin natsuwa bayan shafe shekaru a harkar mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Aisha Buhari ta bayyana cewa ba ta da shirin sake aure bayan rasuwar mijinta, marigayi Muhammadu Buhari.

Wannan bayani ya fito ne a cikin wani sabon littafin tarihin marigayin mai shafuka 600 da aka kaddamar a fadar shugaban kasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana dalilin Buhari na kin goyon bayan takarar Osinbajo a 2023

Aisha Buhari tare da mijinta a fadar shugaban kasa
Aisha Buhari tare da mijinta a fadar Aso Rock Villa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa littafin na dauke da tarihin rayuwar Buhari tun daga yarintarsa a Daura, Jihar Katsina, har zuwa rasuwarsa a wani asibiti a Landan a tsakiyar watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Littafin, wanda Dr Charles Omole ya rubuta, ya bayyana yadda Aisha Buhari za ta yi sabon babi na rayuwarta bayan shafe shekaru takwas a matsayin uwargidan shugaban kasa.

Aisha za ta yi aure bayan Buhari?

A cewar littafin, Aisha Buhari ta bayyana matsayarta, inda ta ce shawarar kin sake aure ba hukunci ba ne da zai shafi wasu mata, illa dai fahimtar halin da take ciki a yanzu.

Littafin ya rawaito kalamanta da cewa:

“Ina da jikoki, kuma miji guda ya isa.”

Marubucin ya yi bayani cewa wannan matsayi nata ya kauce wa ra'ayin wasu 'al’adu da ke kallon mace a matsayin wadda ta ci amanar mijinta idan ta sake aure bayan ya rasu, ko kuma tsarkakakkiya idan ta ki.

Kara karanta wannan

Yadda hadiman Buhari suka so ayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC a zaben 2023

Rayuwar Aisha Buhari bayan barin mulki

Littafin ya nuna cewa Aisha Buhari na shirin rage bayyanar ta a bainar jama’a, za ta raba lokacinta tsakanin kula da iyali, ayyukan jin kai da kuma tafiye-tafiye.

An bayyana cewa tana son kula da jikokinta domin su tuna da ita a matsayin uwa da kakarsu a cikin gidajensu, ba wai a matsayin wata fuska da suke kallo ta cikin gilashin mota ba.

Aisha Buhari tare da marigayi tsohon shugaban kasa
Marigayi shugaba Buhari tare da matarsa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Haka kuma, ta kuduri aniyar ci gaba da gudanar da gidauniyarta da kuma cibiyar kula da cututtukan zuciya da lafiya a Kano, wadda littafin ya ce ta riga ta yi ayyukan jinya fiye da 200.

Rayuwar aure da Aisha ta yi da Buhari

Aisha Buhari, wadda aka haifa a shekarar 1971 a Jihar Adamawa, ta auri Muhammadu Buhari a ranar 2 ga Disamba, 1989, bayan rabuwarsa da tsohuwar matarsa a 1988.

Sun shafe shekaru 35 tare da aure, suna da ‘ya’ya biyar, kuma ta zama uwargidan shugaban kasa ne a shekarar 2015 lokacin da Buhari ya lashe zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Matar Buhari, Aisha ta fadi yadda iyalansa ke rayuwa bayan rasuwarsa

Rayuwar iyalan Buhari bayan rasuwarsa

A wani labarin, kun ji cewa Aisha Muhammadu Buhari ta yi magana game da rayuwar da suke bayan rasuwar mijinta a 2025.

A wata hira da ta yi da manema labarai a Abuja, ta bayyana cewa rayuwa ba ta kasance kamar lokacin da marigayin ke tsakaninsu ba.

Ta kara da cewa mutanen Buhari sun masu ta'aziyya kuma sun cigaba da harkokinsu, ita kuma tana cigaba da kula da 'ya'ya da jikoki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng