Musulunci Ya Yi Rashi: Shugaban Izalah a Gombe, Abdullahi Barde Ya Rasu
- Kungiyar Izalah (JIBWIS) reshen Gombe ta sanar da rasuwar daya daga cikin shugabanninta na kungiyar a Kwamin Yamma
- Shugaban JIBWIS a Gombe, Alhaji Salisu Muhammad Gombe, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, yana bayyana alhininsa
- An gudanar da sallar jana’izar marigayin da misalin karfe 11:00 na safe a masallacin Jumma’a na Bolari, inda aka yi masa addu’o’in rahama
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Kungiyar Izalah reshen Gombe ta sanar da rasuwar daya daga cikin shugabanninta a jihar bayan fama da jinya.
Shugaban Jama'atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah a jihar Gombe, Alhaji Salisu Muhammad Gombe ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar shugaban Izala a Gombe
Hakan na cikin wata sanarwa da shafin JIBWIS Gombe ya wallafa a Facebook a yau Talata 16 ga watan Disambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, kungiyar a madadin shugabanta, ta bayyana alhini kan rashin jajirtaccen malamin Alhaji Abdullahi Barde wanda ya ba da gudunmawa.
Har ila yau, kungiyar ta gayyaci daukacin al'ummar Musulmi zuwa jana'izar marigayin wanda shi ne shugaban JIBWIS Kwamin Yamma.
Sanarwar ta ce:
"Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un.
"A madadin Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe Shugaban ta na Jiha Alhaji Salisu Muhammad Gombe.
"Ana gayyatar sallar jana'iza bisa ga rasuwar Alhaji Abdullahi Barde Shugaban Kungiyar JIBWIS ta Kwamin Yamma."
Yaushe aka yi sallar jana'izar marigayin
Rahotannin sun tabbatar da cewa an yi sallar jana'izar marigayin da misalin karfe 11:00 na safe a masallacin Bolari da ke kwaryar Gombe.
Kungiyar ta yi addu'a ga marigayin da fatan Allah ya jikansa ya gafarta masa ya kuma ba iyalansa hakurin rashi.
"Za a gabatar da sallar janaiza a masallacin Jumma'a na Bolari, yau Talata da misalin karfe 11:00am.
"Muna Addu'ar Allah ya ji ƙansa ya gafarta masa ya sanya Aljannah ta zamto makomarsa in tamu tazo Allah ya sa mu cika da Imani."
- Cewar sanarwar

Source: Original
Abin da ake fada game da marigayin a Gombe
Mutane da dama da suka san marigayin sun bayyana cewa mutum ne mai jajircewa wanda ya sadaukar da rayuwarsa kan ba addinin Musulunci gudunmawa.
Wani mazaunin cikin garin Gombe ya bayyana cewa marigayin mutumin kirki ya san shi sosai kuma suna da alaka mai kyau.
Umar Ibrahim ya ce yawancin 'ya'yan marigayin abokansa ne suna kiransa da Baffa saboda makwabtaka da suke da bayan alakar abokantaka da 'ya'yansa.
Shugaban malaman Izala ya rasu a Gombe
A baya, mun ba ku labarin cewa rahotanni sun nuna cewa malamin Izala, Malam Shu’aibu A Ahmad ya rasu a Gombe bayan doguwar jinya da ya yi a asibiti.
Bayanan sun nuna cewa marigayin yana daga cikin fitattun malaman Izala da suka yi karatu a kasashen waje a jihar Gombe.
Kungiyar Izala ta tabbatar da haka a ranar Litinin, 28 ga Yuli, 2025 wanda aka yi jana’izarsa da misalin karfe 5:00 na yamma a unguwar Jekadafari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

