Kasar Amurka Ta Fitar da Sabon Gargadi game da 'Yan Najeriya

Kasar Amurka Ta Fitar da Sabon Gargadi game da 'Yan Najeriya

  • Ofishin Jakdancin Amurka a Abuja ya gargadi 'yan Najeriya masu amfani da takardun bogi wajen neman izinin shiga kasar
  • Jakadan Amurka da ministan harkokin wajen Najeriya sun tattauna kan dangantakar kasashen biyu da hanyoyin hadin gwiwa
  • Tun a baya dai Amurka ta gargadi jama’a kan ’yan damfara da ke karyar bayar da aiki ko biza ta hanyar biyan kudi ta intanet

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Amurka ta yi gargadi ga ’yan Najeriya kan illar shiga harkar magudin biza, tana mai cewa irin wannan aiki na iya jawo hukunci mai tsanani har da haramcin shiga Amurka na dindindin.

Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja ya bayyana cewa dokokin shige da ficen Amurka ba sa sassauci ga duk wanda aka samu da karya, yana mai kira ga jama’a da su bi hanyoyin doka kawai wajen neman biza.

Kara karanta wannan

Abba ya yi ta maza, ya murkushe yunkurin Ganduje na kafa sabuwar Hisbah a Kano

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Gargadin ya fito ne ta wata sanarwa da ofishin Amurka ya wallafa shafinsa na X, inda ya ja hankalin masu neman biza da su guji bayar da bayanan karya ko amfani da takardun bogi a lokacin cike takardun biza.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gargadin Amurka ga 'yan Najeriya kan biza

A cikin sanarwar, ofishin jakadancin Amurka ya ce magudin biza na da mummunan sakamako a karkashin dokokin shige da ficen kasar.

Sanarwar ta ce:

“Magudin biza zai iya jawo mummunan sakamako. Yin karya ko gabatar da takardun bogi na iya kai wa ga haramcin biza na dindindin a karkashin dokokin shige da ficen Amurka.”

Ya kara da cewa duk bayanan da ake nema daga masu neman biza ana bincikensu ne sosai, kuma duk wata dabara ta karya na iya janyo hukunci da ba za a iya janye wa ba a nan gaba.

Jakadan Amurka ya gana da Ministan waje

Kara karanta wannan

Amurka: Trump ya kwace babbar tankar mai mallakar kamfanin Najeriya

Vanguard ta rahoto cewa gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya gana da ministan markokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar.

A cewar Amurka, ganawar ta mayar da hankali ne kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wuraren da za a kara hadin gwiwa a fannoni daban-daban.

Yusuf Tuggar da jakadan Amurka a Najeriya
Ministan harkokin Najeriya da jakadan Amurka. Hoto: US Mission in Nigeria
Source: Facebook

Sanarwar ta ce Amurka na sa ran ci gaba da aiki tare da Najeriya kan al’amuran da suka shafi moriyar kasashen biyu, ciki har da tsaro, kasuwanci da huldar diflomasiyya.

Gargadin Amurka kan ’yan damfara

A wani gargadi da ya gabata, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ja hankalin jama’a kan yawaitar ’yan damfara da ke karyar zama wakilan daukar ma’aikata ko masu ba da biza.

Ofishin jakadancin ya ce wadannan mutane kan yi alkawarin samar da aiki a Amurka, bizar aiki ko tabbatar da samun gurbin tafiya kasar.

A cewar sanarwar, ofishin ba ya kiran mutane ko tura sakonnin imel domin neman biyan kudin biza ta wasu hanyoyi da ba a amince da su ba, kuma ba ya bayar da tabbacin biza ko aiki saboda biyan kudi.

Kara karanta wannan

'Za a kamo shi,' Benin ta gano kasar da sojan da ya so juyin mulki ya buya

An samu harin 'yan bindiga a Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Amurka ta tabbatar da kai hari kan dalibai a jami'ar Brown, inda aka kashe mutane.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa abin Allah wadai ne kuma za a dauki mataki.

Rundunar 'yan sandan yankin ta fara bincike bayan an sanar da dakatar da karatu da jarrabawar da ake rubuwa a makarantar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng