Bizar shiga Amurka: Kuyi kaffa-kaffa da Atiku, an gargadi Amurka

Bizar shiga Amurka: Kuyi kaffa-kaffa da Atiku, an gargadi Amurka

- Gwamnatin tarayya ta sanar da US da tayi hattara da bawa Atiku tikitin shiga kasar

- Gwamnatin tasan shirye shiryen da yake akan dage dokar hana shi tikitin shiga US

- Mun fahimta kuma munsan cewa US na da damar bawa kowa tikitin shiga kasar ta

"Kuyi kaffa-kaffa da Atiku" - Gwamnatin Tarayya ta gargadi Amurka kan bizar shiga Amurkas

"Kuyi kaffa-kaffa da Atiku" - Gwamnatin Tarayya ta gargadi Amurka kan bizar shiga Amurkas
Source: Facebook

Gwamnatin tarayya ta sanar da US cewa da tayi hattara gurin bawa Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed yace Gwamnatin na sane da take taken tsohon shugaban kasa don samun tikitin da kasar ta haramta mishi.

DUBA WANNAN: Yadda yara suka kashe Mamman Nur, Kwamandan Boko Haram

Duk da US tana da ikon bada tikitin shiga kasar, amma yakamata ta zama a hankalce.

"Muna son US ta zama ba mai bin bangare daya ba kada ta sanya wa mutane tunanin cewa ta aminta da Atiku. Kada US ta nuna tana goyon bayan wani Dan takara akan wani, inji Lai Mohammed.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel