Shugaba Tinubu Ya Yi Wa 'Yan Najeriya Albishir kan Matsalar Rashin Tsro
- Ana ci gaba da fuskantar matsalolin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya wanda hakan ke tayar da hankulan jama'a
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen matsalar
- Mai girma Tinubu ya bayyana shirin da gwamnatinsa ke yi domin cewa kwanciyar hankali ta dawo zukatan 'yan Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na kawo karshe matsalar rashin tsaro.
Shugaba Tinubu ya nuna cewa gwamnatinsa za ta hada dukkan kayan aikin sojoji da hukumomin tsaro domin murkushe barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa a fadin Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jihar Legas, ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025 yayin da ya bude taron shekara-shekara na babban hafsan sojojin kasa na 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Bola Tinubu ya ce kan rashin tsaro?
Mai girma Tinubu wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilta, ya sake tabbatar da cewa tsaro na daga cikin manyan ginshikan manufar gwamnatinsa ta Renewed Hope, jaridar Thisday ta dauko labarin.
Shugaban kasar ya kuma sanar da sayen motocin yaki masu kariya daga nakiyoyi, da sababbin motocin yaki masu sulke ga sojoji, tare da gyaran fiye da motoci 100 na yaki masu sulke.
“Babu wata kasa da za ta samu daukaka ba tare da tsaro ba. Wannan gwamnati ta kuduri aniyar hada dukkan kayan aikin sojoji da hukumomin tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin dukkan ’yan Najeriya."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa zai zamanantar da rundunar sojoji
Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa na da cikakken kuduri wajen zamanantar da rundunonin sojojin Najeriya ta hanyar inganta horaswa, samar da kayan aiki na zamani da kuma kara karfin gudanar da ayyuka.
Ya ce baya ga shigar da jiragen sama masu saukar ungulu cikin rundunar sojojin kasa da kuma horas da matuka jirgi, gwamnati ta ci gaba da sayen karin motocin MRAP, motocin yaki masu sulke da motocin sintiri domin kara kare sojoji da inganta tasirin su a fagen daga.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya yabawa sojoji
Da yake yabawa rundunar sojojin kasa ta Najeriya kan nasarorin da ta samu a yaki da ta’addanci da sauran kalubalen tsaro, Shugaba Tinubu ya ce rahotanni na nuna kyakkyawan sakamako kan ayyukan jami'anta.
Ya ce ana samun nasarorin ne a dalilin kwarewa, jarumtaka da kuma hadin gwiwar ayyuka tare da sauran hukumomin tsaro.
Shugaban ya tabbatar wa sojoji da cikakken goyon bayan gwamnati wajen cika nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu na kare Najeriya, yana mai jaddada cewa tsaro na daga cikin manyan fannoni takwas da gwamnatinsa ta ba fifiko.
Jami'an tsaro sun kashe jagoran 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka wani hatsabibin jagoran 'yan bindiga a jihar Sokoto.
Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka jagoran 'yan bindigan ne mai suna Kachalla Na'Allah a karamar hukumar Isa.
Majiyoyi sun bayyana cewa harbe tantirin jagoran 'yan bindigan ne yayin da jami’an tsaro suka tare shi a tsakanin kauyukan Girnashe da Kuka Tara, a gundumar Tsabre ta karamar hukumar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

