Shugaban Ƙasa, Gwamnoni da Ciyamomi Sun Raba Naira Tiriliyan 1.92 a Watan Nuwamba
- Kwamitin FAAC ya raba jimillar Naira tiriliyan 1.92 a tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a watan Nuwamban 2025
- An raba wannan kuɗi ne duk da samun raguwar harajin VAT, wanda ya ragu da Naira biliyan 156.78 idan aka kwatanta da watan Oktoba
- Jihohi masu arzikin ma’adinai sun samu Naira biliyan 134.35 a matsayin kashi 13 da ake ba su na kuɗin da albarkatunsu ke kawo wa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja - Kwamitin raba kuɗin asusun tarayya (FAAC) ya sanar da raba jimillar Naira tiriliyan 1.92 ga Gwamnatin Tarayya, jihohi da kananan hukumomi a watan Nuwamba.
Rahoton kwamitin ya ce an yanke shawarar raba kudin ne a taron FAAC na watan Disamba ta shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja, karkashin jagorancin Doris Uzoka-Anite, Karamar Ministan kuɗi.

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito a cewar sanarwar taron, kudin da aka raba sun ƙunshi N1.40tr daga kudin shari’a, N485.83bn daga harajin kaya (VAT), da kuma N39.64bn daga harajin canja wurin kuɗi ta lantarki (EMTL).
FAAC ya yi rabon kuɗi ga gwamnatoci
FAAC ya ce jimillar kudin shiga da aka samu a watan Nuwamba ta kai Naira tiriliyan 2.34. Daga ciki, an cire N84.25bn a matsayin kudin tattara haraji.
Sanarwar bayan taron ta ƙara da cewa a gefe guda kuma, an samu Naira biliyan 330.62bn daga kuɗin da ake adanawa a banki da sauransu.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“An karɓi N1.736tr a matsayin kudin shari’a a watan Nuwamba 2025, wanda ya ragu da N427.969bn idan aka kwatanta da N2.164tr da aka samu a watan Oktoba 2025.
Kudin VAT sun ragu a Nuwamba
FAAC ya bayyana cewa jimillar kudin VAT da aka samu a watan Nuwamba sun kai N563.04bn, abin da ke nuna raguwa da N156.78bn daga N719.82bn da aka raba a watan Oktoba.
Daga wannan adadi, an ware N22.52bn a matsayin kudin tattara VAT. Daga cikin N1.92tr da aka raba gaba ɗaya, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 747.15.
Jihohi kuma sun karɓi Naira biliyan 601.73, yayin da kananan hukumomi suka samu Naira biliyan 445.26. An kuma ba wa jihohi masu albarkatun kasa N134.35bn.

Source: Facebook
Dangane da Naira tiriliyan 1.40 na kudin shari’a, FAAC ta ce Gwamnatin Tarayya ta karɓi N668.33bn, jihohi sun samu N338.98bn, kananan hukumomi kuma N261.35bn.
Daga Naira biliyan 485.84 na harajin VAT, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 72.88, jihohi Naira biliyan 242.92, kananan hukumomi Naira biliyan 170.04.
A bangaren EMTL, Tarayya ta karɓi Naira biliyan 5.95, jihohi sun karɓi Naira biliyan N19.82 , kananan hukumomi kuma sun samu Naira biliyan 13.88 a rabin.
Kuɗin da gwamnatoci suka raba ya karu
A baya, kun ji cewa gwamnatin Tarayya, gwamnonin jihohi da kananan hukumomi sun karɓi jimillar N1.72tr daga rabon kudin Asusun Tarayya (FAAC) na watan Nuwamba, 2024.
Wannan ya biyo bayan zaman rabon kason da aka saba gudanarwa na kwamitin FAAC, inda aka raba kudin shiga ga bangarorin gwamnati uku - tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
A cewar bayanan da suka fito daga ma’aikatar tattalin arziki ta kasa, an bayyana cewa a karshen watan Nuwamba, Naira tiriliyan 3.14 ne suka shigo cikin asusun tarayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


