Gwamna Uba Sani Ya Dora Wa Kansa Nauyi da Ya Kai Ziyara Gidan Sheikh Dahiru Bauchi
- Gwamna Uba Sani ya jagoranci tawagar gwamnatin Kaduna zuwa gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin yin ta'aziyya
- Sanata Uba Sani ya ce gwamnatin Kaduna za ta karrama marigayi Dahiru Bauchi saboda irin gudummuwar da ya bada rayuwarsa
- Gwamnan ya yi alkawarin kafa gidauniya ta musamman da za ta ci gaba da wasu ayyukan alherin da babban malamin ya saba aiwatarwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi alkawarin kafa wata gidauniya domin tunawa da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Uba Sani ya ce gudauniyar za ta rika gudanar da ayyukan alheri kamar wa’azin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai, abin da marigayin ya shahara da shi a rayuwarsa.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Gwamna Uba Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Uba Sani ya je ta'aziyya Bauchi
Uba Sani ya yi wannan alkawari na abin alheri a ranar Lahadi, lokacin da ya jagoranci wata tawaga mai mutum 30 zuwa ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Dahiru Bauchi.
Da yake jawabi yayin ziyarar, ya ce gwamnatin Kaduna za ta kafa wani kwamiti da zai kunshi ‘ya'yan marigayi Sheikh, dalibansa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tsara cikakkun bayanan kafa gidauniyar.
Gwamnan ya jaddada cewa duk da marigayi dan Jihar Bauchi ne, amma Kaduna za ta girmama shi fiye da kowa, la’akari da gudummawar da ya bayar ga Musulunci, shugabanci da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Za a kafa gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi
A cewarsa, gidauniyar da za a kafa ba kawai za ta ci gaba da ayyukan alheri da marigayi malamin addini ya fara ba, har ma za ta aiwatar da tsare-tsaren da ya yi niyyar yi.
Uba Sani ya ce:
“Na kan tuntubi marigayi malamin mu, kuma duk shawarar da ya ba ni tana haifar da sakamako mai kyau. Ni ina cikin iyalan marigayi Sheikh, kuma muna da kyakkyawar alaka da iyalansa.”
“Za mu ci gaba da kokarinsa na hada kan Musulmi da kuma tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin mabiya addinai daban-daban, ba a Jihar Kaduna kadai ba, har ma a fadin kasar nan baki daya.”
Iyalan Dahiru Bauchi sun yabi Uba Sani
Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Khalifa Sayyid Ibrahim Dahiru Bauchi, ya ce Uba Sani ya dade yana da kusanci da mahaifinsu tun kafin ya zama gwamnan Jihar Kaduna.
Sayyid Ibrahim ya ce:
“Nan gidanku ne. Bayan sanar da rasuwar malam, mun yi magana ta waya. Haka kuma ka turo wakilai da suka halarci sallar jana’iza, sannan daga baya ka sake turo wata tawagar malamai domin yi mana ta’aziyya.
“Yau kuma ka zo da kanka domin yi mana jaje. Wannan yana nuna girman da ka ke bai wa marigayi Sheikh. Allah (SWT) Ya saka maka da alheri, Ya kuma biya maka bukatun zuciyarka.”

Source: Facebook
Khalifa Sayyid Ibrahim ya kuma gode wa Gwamna Uba Sani, a madadin ‘ya’ya 82 na marigayin, bisa alkawarin da ya yi na sake gina gidan kakansu, inda marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya taso, in ji Daily Trust.
Tawagar Katsina ta je gidan Dahiru Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa Malam Dikko Umar Radda ya jagoranci tawagar manyan jiga-jigai daga Katsina zuwa wurin ta'aziyyar Sheikh Dahuru Usman Bauchi.
Mai girma Gwamna Dikko Radda ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga musulmai da Najeriya baki ɗaya.
Dikko Radda ya shiga cikin gida, ya ziyarci matan marigayin ɗaya bayan ɗaya, domin yi masu ta’aziyya tare da alkawarin ci gaba da taimaka masu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


