"Yana Kaunar 'Yan Najeriya," Tinubu Ya Tuno da Wasu Abubuwa 4 game da Buhari

"Yana Kaunar 'Yan Najeriya," Tinubu Ya Tuno da Wasu Abubuwa 4 game da Buhari

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin abin koyi saboda gaskiya, rikon amana da kaunar 'yan kasa
  • Tinubu ya ce abin koyi da Buhari ya bari ba mukamai ko ayarin motoci ba ne, illa gaskiya, saukin kai da daukar mulki a matsayin amanar jama’a
  • Shugaban ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da aikin da Buhari ya fara domin mutunta tarihinsa da kuma gina kasa mai adalci a nan gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tuno da kyawawan halaye na marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

A taron kaddamar da littafin tarihin rayuwar Buhari a Abuja, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin abin koyi, mai tsantsini, gaskiya da yi wa jama'a hidima.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi

An kaddamar da littafin rayuwar Buhari a Abuja.
Shugaba Bola Tinubu ya tuno da rayuwar Muhammadu Buhari a wurin kaddamar da littafinsa a Abuja. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Tinubu ya tuno da rayuwar marigayi Buhari

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wajen taron, inda ya ce halartar taron babban abin alfahari ne a gare shi, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta ruwaito cewa Buhari ya rasu ne a ranar 13 ga Yulin 2025 yana da shekaru 82 a wani asibiti da ke birnin Landan bayan fama da doguwar jinya.

An dawo da gawarsa Najeriya inda aka yi masa jana’iza a garinsa na Daura, jihar Katsina, wanda ya samu halartar shugabannin kasashe daban-daban.

A wajen taron kaddamar da littafin, Tinubu ya mika sakon ta’aziyya da goyon baya ga iyalan Buhari, inda ya ce:

“Ina mika gaisuwar ta’aziyyar al’ummar Najeriya ga uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ’ya’yanta da jikokinta. Allah Ya ba ku hakurin jure wannan rashi, kuma ku sani cewa addu’o’in Najeriya na tare da ku, kuma sunan Buhari zai ci gaba da wanzuwa har karni mai zuwa.”

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa, Gowon ya mutu? Hadiminsa ya fito da gaskiya

Alakar siyasar Buhari da Tinubu a 2014

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban kasar ya tuno da irin rawar da Buhari ya taka, yana mai cewa:

“Ana auna tasirin shugaba ba wai da mukaman da ya rike ko ayarin motocin da ya hau ba ne. Ana aunawa ne da irin baya mai kyau da ya bari bayan gama hidimtawa al'umma.
"Hakika, Shugaba Muhammadu Buhari ya bar baya mai kyau, kuma kowa ya kira sunansa zai ce 'baba mai gaskiya', ya gudanar da rayuwa mai sauki da akidar cewa mukamin gwamnati amana ne, ba ganima ba.”

Tinubu, wanda ya yi doguwar tafiyar siyasa tare da Buhari, ya tuna yadda suka gina kawancen siyasa, yana mai cewa:

“Tare muka gina babban kawance, muka zagaya kasar nan muna yakin neman zabe, muka kuma tabbatar cewa Najeriya na iya samun sauyi.
"Wannan hadaka ta hada ra’ayoyi daban-daban a wuri daya, kuma ta kai ga nasarar da ta shiga tarihi a 2015, inda muka hambarar da shugaban kasa mai-ci a wancan lokaci.”

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan matsalolin Najeriya

Gwamnoni, Aisha Buhari da sarakuna sun halarci bikin kaddamar da littafin Buhari
Aisha Buhari gwamnoni, sarakuna da kusoshi sun halarci bikin kaddamar da littafin Buhari a Abuja. Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

Manyan abubuwa 4 na tunawa da Buhari

Shugaban kasar ya kuma yi tsokaci kan ci gaban jam’iyyar APC, yana cewa:

“Kawancen da muka gina a 2014 yanzu ya zama jam’iyyar siyasa mafi saurin girma a Afirka. Kuma tana ci gaba da bunkasa.”

Tinubu ya bayyana manyan ginshikai hudu da za a rika tunawa da Buhari da su da suka hada da saukin kai, tsaro, hangen nesa da adalci na zamantakewa.

Har ila yau, ya yabawa Buhari kan jajircewarsa wajen tallafawa marasa karfi, yana mai cewa:

“Ya yi imani da tsare-tsaren tallafin jama’a domin tabbatar da cewa gwamnati ba ta manta da talakawa da masu rauni ba. Ba shakka, yana kaunar 'yan Najeriya.”

A karshe, Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba daga inda Buhari ya tsaya, yana mai cewa hakan ne zai sa tarihi ya ci gaba da tunawa da tsohon shugaban kasar.

Tinubu ya ziyarci iyalan Buhari a Kaduna

Kara karanta wannan

Ganduje na fuskantar barazanar shari'a game da yi wa Hisbah kishiya a Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaban Bola Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansu da ke cikin Kaduna.

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Hajiyan Aisha Buhari da sauran iyalan marigayin cewa gwamnatinsa za ta dora daga ayyukan da Buhari ya bari.

Shugaban kasa Tinubu ya kai wannan ziyara ne yayin da ya je Kaduna domin halartar daura auren dan tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com