Ministan Tsaro Ya Tsage Gaskiya kan Matsalar Rashin Tsaro a Najeriya

Ministan Tsaro Ya Tsage Gaskiya kan Matsalar Rashin Tsaro a Najeriya

  • Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi tsokaci kan matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a Najeriya
  • Janar Christopher Musa ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta fi karfin wani mutum guda ya ce zai iya kawo karshenta
  • Tsohon hafsun sojojin ya kuma bayyana cewa karfin 'yan bindiga, 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuffuka ya ragu sosai

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya jaddada cewa tunkarar kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta na bukatar hadin kai.

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa babu wata runduna ko mutum guda da zai iya magance wadannan matsaloli shi kadai.

Christopher Musa ya yi magana kan rashin tsaro
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Janar Musa ya fadi hakan ne a wajen taron shekara-shekara na hafsan sojojin kasa na 2025, wanda aka gudanar ranar Litinin, 15 ga watan Disamba a dakin taro na Nebo, barikin Abalti da ke jihar Legas.

Kara karanta wannan

Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan tsaro ya yaba wa nasarar sojoji

Ministan ya ce nasarorin da aka samu sun samo asali ne daga jarumtakar sojoji, ingantaccen tsari da aiwatarwa, tare da karuwar tasirin hadin gwiwar ayyuka da ake gudanarwa karkashin tsarin aiki tare na rundunoni da hukumomi da dama.

Ya kuma bayyana cewa karfin ayyukan kungiyoyin ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran miyagun laifuffuka ya ragu sosai a fannoni daban-daban na ayyukan tsaro a fadin kasar, shafin Zagazola ya dauko labarin.

Janar Musa ya yi tsokaci kan rashin tsaro

“Gaskiyar magana ita ce, babu wata runduna, hukuma ko mutum guda da zai iya fuskantar kalubalen tsaro na yau shi kadai."
“Ci gaba da samun nasara zai tabbata ne kawai ta hanyar hadin kai, ayyukan sojoji a hade, musayar bayanan sirri, tsara aiki tare da kuma kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro."
“Yayin da muke neman nasarar ayyukan tsaro, bai kamata mu manta da muhimmancin bangaren jin kai da rayuwar sojoji ba."

Kara karanta wannan

'Yana kan daidai': Gumi ya goyi bayan Matawalle, ya fadi tasirinsa a Zamfara

- Janar Christopher Musa

Ministan tsaro ya yabi taron da aka shirya

Janar Musa ya kara da cewa taron na ci gaba da zama muhimmin dandali ga rundunar sojojin kasa ta Najeriya, domin duba matsayin ayyukanta, tantance shirinta da kwarewarta, tare da daidaita alkiblarta kan manyan manufofin tsaron kasa.

“Ba za a iya raina muhimmancin wannan taro ba, musamman idan aka yi la’akari da sarkakiya da canjin yanayin tsaro da kasar nan ke fuskanta."
“Najeriya na ci gaba da fuskantar ta’addanci, bore, ’yan bindiga da sauran barazanar tsaro, wadanda ke bukatar mai da hankali na dogon lokaci, fahimtar manufa da shugabanci mai iya sauyawa da yanayi."

- Janar Christopher

Janar Christopher Musa ya yi maganganu kan matsalar rashin tsaro
Janar Christopher Musa (mai ritaya) wanda ke rike da kujerar Ministan tsaro Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Ministan ya ce ma’aikatar tsaro za ta ci gaba da bayar da jagoranci, goyon bayan manufofi da bunkasa kwarewa domin tabbatar da cewa rundunonin sojojin Najeriya sun kasance masu kwarewa da saurin daukar mataki.

Ya kuma ce za a kara karfafa tsare-tsaren hukumomi da ke inganta rikon amana da nagarta wajen aiki.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara bayan sun gwabza fada da 'yan bindiga a Sokoto.

Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe ’yan bindiga 11 tare da kwato manyan makamai da dama daga hannunsu.

Sojojin dai sun samu nasarar ne lokacin da suka shiryawa 'yan bindigan kwanton bauna bayan sun samu sahihan bayanai kan motsinsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng