"Karya Kake Yi," Tsohon Gwamnan Sakkwato Ya Maida Martani Mai Zafi ga Bello Turji
- Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya nesanta kansa daga zargin hannu a rura wutar ta'addanci a Arewa
- Bafarawa ya karyata kalaman da kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji ya yi cewa yana cikin masu taimaka wa 'yan bindiga
- Ya ce Turji ya ambaci sunansa ne domin faranta wa wadanda suka dauki nauyinsa, yana mai tambayar shekarunsa nawa lokacin da ya mulki Sakkwato
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya fito ya kare kansa daga zargin hannu a taimakawa 'yan bindiga a Arewacin Najeriya.
Tun farko hatsabibin dan bindigar nan, Bello Turji ya zargi Bafarawa da wani tsohon gwamnan Zamfara da hannu a rura wutar rashin tsaron da ta addabi Arewa.

Source: Twitter
Bafarawa ya yi fatali da zargin Bello Turji

Kara karanta wannan
Bayan ganin bidiyon Bello Turji, APC ta hango dalilin alakanta Matawalle da 'yan bindiga
Sai dai Bafarawa, wanda ya mulki Sakkwato tsakanin 1999 zuwa 2007, ya shaida wa Vanguard ta waya cewa bai taba goyon bayan kowanne nau’in tashin hankali ko ta'addanci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya yi mamakin ikirarin Bello Turji, inda ya ce babu abin da ake kira ‘yan bindiga ko ta’addanci a Sakkwato da Zamfara lokacin da ya bar ofis a 2007
Bafarawa, wanda yana daya daga cikin wadanda suka kafa PDP kuma ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2007, ya ce Turji ba ya cikin hayyacinsa, watakila a mafarki ya ambaci sunansa.
Martanin Bafarawa kan zargin hannu a ta'addanci
Ya ce akwai ayar tambaya kan dalilin da zai sa dan ta'addan ya ambaci sunansa a cikin masu taimaka wa ta'addanci kusan shekaru 20 bayan ya sauka daga mulki.
“Ina Bello Turji yake a lokacin da nake gwamnan Jihar Sakkwato, kuma ya na dan shekaru nawa a wancan lokacin? Ban taba hulɗa da shi ba, kuma har yanzu babu abin da ya taba hada ni da shi.
"Me zan samu daga ‘yan bindiga ko ta’addanci a shekaruna? Abin mamaki ne mutum irin wannan zai shirya karya ya jingina mini. Wasu mutane ke amfani da shi domin su mini kage.
"Ni mutum ne da ke kishin zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihohi na da Najeriya, kuma ba zan taba shiga wani abu da zai kawo rashin kwanciyar hankali ba."
- Attahiru Bafarawa.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa zargin da Bello Turji ya yi ba shi da tsuhe, illa dai ya ambaci sunansa ne domin farantawa wadanda suka dauki hayarsa ya mini karya, in ji rahoton Punch.
Bello Turji ya yi magana kan zargin Matawalle
A wani rahoton, kun ji cewa hatsabibin 'dan bindiga, Bello Turji ya fito da wani sabon bidiyo inda ya ke karyata zargin cewa Matawalle ya ba su miliyoyi.
Hakan ya biyo bayan zargin da tsohon hadimin Matawalle, Musa Kamarawa ya yi cewa tabbas akwai alaka tsakanin tsohon mai gidansa da yan ta'adda.
A faifan bidiyon da ya saki, Bello Turji ya ce ba wai kare Bello Matawalle yake yi ba, hasalima, babu wanda ya tsana kamarsa saboda a mulkinsa ya cutar da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
